Gwamnatin Jihar Yobe ta umarci dukkanin makarantun firamare da sakandare na jihar da a rufe su daga ranar 31 ga watan Yuli saboda zanga-zangar da ake shirin yi a fadin kasar nan kan wahala da yunwa.
Umarnin na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan ilimi na jihar, Farfesa Abba Idriss, ya fitar tare da sanya hannun daraktan kula da makarantu, Bukar Modu a Damaturu.
- Don Hana Zanga-Zanga, Shugaba Tinubu Ya Amince Da Kafa Ofishin Matasa A Abuja
- Arsenal Ta Kammala ÆŠaukar Riccardo Calafiori Daga Bologna
“Mai girma kwamishina, Farfesa Abba Idriss Adam ne, ya umarce ni da na rubuto tare da sanar da ku amincewarsa na rufe dukkanin makarantun Firamare da Sakandare a jihar.
“Duk da haka, bisa la’akari da abubuwan da ke faruwa, makarantun jihar za su kasance a rufe daga ranar Laraba 31 ga watan Yuli, 2024,” in ji Modu.
Sanarwar ta kuma umarci makarantu da su koma gudanar da harkokin ilimi a ranar Lahadi 15 ga watan Satumba, 2024.