Kamfanin sadarwa na MTN ya rufe ofisoshinsa da ke fadin Nijeriya a yau Talata.
Matakin kamfanin ba ya rasa nasaba da yadda wasu abokanan huldarsa da aka rufewa layin waya suka yi cincirindo a ofisoshin kamfanin har ma wasu suka yi kokarin kutsa kai don neman a bude masu layukan nasu.
- Zanga-Zanga: Gwamnatin Yobe Ta Bayar Da Umarnin Rufe Makarantun Jihar
- Ba Zamu Lamunci Zanga-Zangar Tashin Hankali Ba – IGP
MTN ya rufe layukan mutane saboda sun gaza hada lambarsu ta dan kasa da layinsu.
Talla
MTN ya wallafa sanarwar rufe ofisoshin nasa a shafinsa na X (twitter), inda ya ce “ku sani cewa ofisoshinmu a fadin Nijeriya za su kasance a rufe yau 30 ga watan Yulin 2024.”
Talla