A wani kakkausan kira na wanzar da zaman lafiya, Shugaban Ma’aikatan jihar Kebbi, Alhaji Sifiyanu Garba Bena, ya bukaci matasa da ma’aikata a Nijeriya da su guji shiga ayyukan ‘yan daba a yayin gudanar da zanga-zangar da ake shirin gudanar wa a fadin Nijeriya.
Da yake jawabi ga manema labarai a safiyar ranar Alhamis a ofishinsa da ke Birnin Kebbi, Shugaban ma’aikatan jihar, Alhaji Sifiyanu Garba Bena ya jaddada cewa, duk da cewa zanga-zangar lumana hakki ne da tsarin mulki ya tanada, amma bai kamata a yi barna ko tada fitina a tsakanin al’umma ba.
- Zanga-zanga-zanga: Tinubu Ya Yi Taron Gaggawa Da Manyan Sarakunan Gargajiya A Abuja
- Zanga-zangar Matsin Rayuwa: Gwamnoni Sun Gana Da Ribadu Kan Sha’anin Tsaro
“Mun amince da mutunta ‘yancin matasanmu na bayyana damuwarsu ta hanyar zanga-zangar lumana, amma muna yin Allah-wadai da duk wani nau’i na tashin hankali, lalata dukiyoyin jama’a ko ta gwamnati, da duk wani aiki da zai iya rikidewa zuwa rikici tsakanin al’umma.” In ji Bena
Wannan kiran na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun tashe-tashen hankula bayan zanga-zangar baya-bayan nan da ta rikide zuwa tashe tashen hankula, lamarin da ya janyo hasarar dimbin ababen more rayuwa na gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu.
Don haka, ana kara nuna damuwa kan illar da ka iya haifar da tarzoma ga zaman lafiya da hadin kan al’umma a fadin Nijeriya.
Alhaji Sifiyanu Garba Bena ya bukaci masu ruwa da tsaki musamman wadanda suka shirya zanga-zangar da su ba da fifiko wajen fadin albarkacin bakinsu tare da kaucewa ayyukan da za su kawo cikas ga tsaro da zamantakewar al’umma a jahohin Nijeriya.
Ya kuma tabbatar wa da jama’a cewa jami’an tsaro sun shirya tsaf domin kare lafiyar jama’a tare da mutunta ‘yancin ‘yan kasa.
“Muna aiki kafada da kafada da jami’an tsaro domin ganin an samar da isassun matakan kare rayuka da dukiyoyi a yayin zanga-zangar,” in ji shi.