Tsohon dogarin tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Marigari Sani Abach, Ham-za Al-Mustapha, ya ce duk da yadda ‘yan Nijeriya suka fusata na kiraye-kirayen kan cewa sojojo karbe mulki a Nijeriya, mulkin soja ba mafita ba ce.
Al-Mustapha, wanda ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan halin da kasar ke ciki, ya ce akwai bukatar a daidaita tsarin dimoku-radiyyar Nijeriya domin tunkarar kalubalen da ake fuskanta.
- Lallai A Hukunta Waɗanda Suka Kai Mamaya Ofishin NLC – TUC
- Yadda Aljanu Suka Shiga Zanga-zangar Da Aka Yi A Kano – Dakta Kachako
Ya ce kamata ya yi sojoji su kasance masu bin tsarin dimokuradiyya bisa kwarewa, yana mai jaddada bukatar karfafa sojoji a matsayinsu na wani bangare mai da hankali kan inganta tsaro a kasar nan.
Ya ce, “Sojoji wani bangare ne na dimokuradiyya bayyananne kamar yadda duni-ya take a yau. Amma idan kana da tsarin dimokuradiyya, irin wanda muke aiki da shi na tsarin shugaban kasa. A cikin abubuwan da muka gabatar a baya, ina ada-wa da tsarin shugaban kasa a Nijeriya, misalan da na bayar shi ne, yadda kasashe biyu na kud-da-kud, mafi kusa da mu, wato Ingila da Amurka, daya na tafiyar da tsarin majalisar dokoki, dayan kuma na tafiyar da tsarin shugaban kasa, duk suna da alaka ne da tarihinsu, tare da saukaka wa jama’a, wanda Nijeriya take kwaikwayo.
“Mun kwafi tsarin majalisa, mun canza shi zuwa tsarin shugaban kasa. Dukansu biyun bakon al’ada ne ga al’adunmu, ga tarihinmu, ga asalinmu, fahimtarmu a matsayinmu na al’umma, ta yaya za ku kawo tsari iri daya ku karbe irin naku? ba zai yi aiki ba, zai zama abin kyama.
“Na ba ku wasu misalai, wasu ‘yan siyasa ne suka zo wurina suka ce ka da na fadi haka a fili, ku bari mu ci gaba da gudanar da ayyukanmu kamar yadda muke, amma kuma ni ba zan iya yin wani yaudara ba. Na ce kasar Amurka kasa ce da bakin haure suka zama ‘yan kasa, suna da dokokin da za su kare su kuma tam-bayar da na yi ita ce, a Nijeriya ye dan ci-rani kuma ye asalin dan kasa ne?
“Ta yaya za ku sami tsarin mulki wanda zai kare bakin haure? Wane ne bako a Ni-jeriya? Dukanmu ‘yan kasa ne. Don haka, ya kamata mu tsara tsarinmu da kanmu ba kaikwayon na wasu kasashe ba, dole ne mu sami tsarin dimokuradiyyar da za ta dace da mu. Abin da nake kira kenan a samar, amma batun mulkin soja.”
Sai dai ya ce matasan Nijeriya da suke daga tutocin kasar Rasha sun yi haka ne domin neman mafita, inda suka bukaci da a sake duba hanyar shugabanci domin samun damar magance matsalolin da suke fuskanta.
Al-Mustapha ya ci gaba da cewa shi ba ya goyon bayan zanga-zangar da ake yi a titunan kasar, amma ya jaddada cewa abin da ke da kyau shi ne masu zanga-zangar sun ba da sanarwa kuma duk da dogon sanarwar da suka bayar gwamnati ta kasa biya musu bukatocinsu.