Shugaban hukumar tsaro ta NSCDC, Dr. Audi, ya umarci a rarraba jami’ai 30,000 a duk faɗin ƙasa kafin zanga-zangar da aka shirya gudanarwa daga ranar 1 zuwa 10 ga Agusta. A cikin taron gaggawa da aka gudanar a Shalƙwatar NSCDC a Abuja, Dr. Audi ya jaddada buƙatar jami’an su kasance masu ƙwarewa da ladabi da kuma bin ƙa’idojin.
Ya jaddada cewa yayin da ‘yan ƙasa ke da haƙƙin yin zanga-zanga cikin lumana, ba su da haƙƙin lalata kadarorin gwamnati. Jami’an da za a tura za su kasance ƙarƙashin kulawar shugabannin yanki da kwamandojin Jihohi a jihohi 36 da FCT.
- Zanga-Zanga: Sojoji Sun Karɓe Iko Da Tsaron Hanyar Shiga Abuja
- Ba Zamu Lamunci Zanga-Zangar Tashin Hankali Ba – IGP
Dr. Audi ya gargaɗi jami’an da su guji duk wani aiki na zalunci ko take haƙƙin ɗan adam, yana jaddada cewa NSCDC ba za ta lamunci duk wani abu da zai ɓata sunanta ba. Ya bayyana muhimmancin kare muhimman kadarorin ƙasa da gine-ginen gwamnati daga yiwuwar lalata su yayin zanga-zangar.
Bugu da ƙari, Dr. Audi ya yi kira ga matasan Nijeriya da su guji ayi amfani da su wajen aikata duk wani mummunan aiki, yana ba da shawarar tattaunawa maimakon ayyukan assha da za su jawo da na sani. Ya jaddada aniyar hukumar na haɗa kai da sauran hukumomin tsaro don tabbatar da zaman lafiya da ƙarfafa tsarin tsaron ƙasa.
A cikin jawabin sa, Dr. Audi ya yi kira da a yi zanga-zangar cikin lumana idan dole sai an yi, yana tunatar da zanga-zangar baya da ta haifar da tashin hankali, da lalata dukiya, da kuma rasa rayuka.
Ya umarci jami’ai da su tabbatar zanga-zangar ta kasance cikin lumana kuma su kare gine-ginen gwamnati daga ‘yan daba. Shugaban NSCDC ya tabbatar da cewa hukumar tana da ƙwazo wajen kare rayuka da dukiyoyin ‘yan ƙasa, tare da inganta zaman lafiya da kuma bunƙasa tsaron ƙasa.