Zanga-zanga ta barke a Jihar Katsina, jim kadan bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da ayyuka.
Ganau sun shaida wa Leadership Hausa cewa, tafiyar shugaban kasa daga Kofar-Kaura ke nan, wasu fusatattun matasa suka kau kan titi suna ambaton “Ba ma yi, ba ma yi” abin da ke nuni da cewar matasan na fusace da gwamnatin Buhari.
- Ana Zargin Sojoji Da Kisan Fulani Makiyaya 39 A Nasarawa
- NDLEA Ta Kwace Kwaya Ta N1.5bn Da Cafke Mutum 1,078 Masu Safarar Kwaya A Kano.
Wani ya bayyana cewa, “Sunana Mustapha Muhammad Boss, bayan da shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya kaddamar da aikin wasu mutanen da ba a san ko su waye ba suka fito daga cikin unguwannin da ke kusa da wajen suka yi ta fadin ‘Ba mu yi’ tare da jifan motocin jami’an tsaro da na motocin da ke dauke da tutar APC hadi da kona tayoyi.
“Kan wannan dalilan, muka yanke shawarar kulle shagunanmu domin tsira da lafiyarmu da dukiyarmu. Wannan abin takaici ne kuma ba a abu ne da za a lamunta ba.”
Ko da yake ‘yansanda sun tarwatsa masu zanga-zangar da barkonon tsohuwa yayin da kuma zaman lafiya ya dawo yankin, inda shi kuma Buhari ya sake nausawa wani yankin domin kaddamar da wasu ayyuka a jihar.
LEADERSHIP ta rawaito cewa shugaba Buhari ya ziyarci Katsina ne domin ziyarar aiki ta kwanaki biyu da ya fara a ranar Alhamis.