Mazauna garin Ondo da ke karamar hukumar Ondo ta Yamma a Jihar Ondo, sun mamaye wasu manyan titunan jihar, inda suka yi zanga-zanga kan karancin sabbin takardun kudi da kuma yadda bankunan jihar ke kin karbar tsoffin takardun kudi a fadin jihar.
Masu zanga-zangar wadanda akasarinsu matasa ne, sun yi tattaki domin gudanar da zanga-zangar ta lumana.
- Jam’iyyar LP Ta Kori Dan Takarar Gwamnanta Na Kano, Bashir I. Bashir Daga Jam’iyyar
- Tsoffin Kudi: Kotun Koli Ta Dage Sauraren Shari’ar Zuwa 22 Ga Fabrairu
Har ila yau, masu zanga-zangar sun kuma yi tare wata a tashar mota da ke Akure, inda zanga-zangar ta haifar cunkoson ababen hawa.
Masu zanga-zangar sun kuma kona tayoyin mata a kan hanya, inda jami’an ‘yansanda ke ci gaba da sa ido kan yadda zanga-zangar ke tafiya.
Har ila yau, a garin Ilorin da ke Jihar jihar Kwara, wasu mazauna yankin sun fito don gudanar da zanga-zangar a kan wasu janyoyin jihar tare da kuma datse hanyoyin, inda suka nuna bacin ransu kan karancin sabbin takardun kudi da kuma yadda ‘yan kasuwa a jihar ke kin karbar tsoffin takardun kudi.
Haka lamarin ya ke a Jihar Delta, inda zanga-zangar ta lumana ta barke, inda aka dinga kone-kone, inda masu zanga-zangar suka banka wa injin cire kudi na ATM wuta saboda karancin sabbin takardun kudaden.