Jam’iyyar PDP, ta ce Shugaba Bola Tinubu sam bai damu da halin ‘yan kasar ke ciki ba duk da zanga-zangar da ake gudanarwa.
A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Lahadi, wadda ta samu sa hannun sakataren yada labarunta na kasa, Debo Ologunagba, PDP ta ce jawabin Tinubu ya nuna yadda karara APC da shugaba Tinubu ba su damu da halin kunci da al’ummar kasar ke ciki ba.
- Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Kasuwar Dodoru A Jihar Kebbi, Rumfuna Da Yawa Sun Lalace
- Da Dumi-Dumi: Matasa Sun Daka Wasoson Kayayyaki A Gidan Gwamnatin Bauchi Da Ke Azare
Zanga-zangar wadda ta fara a ranar Alhamis ta rikide zuwa rikici a wasu jihohi, lamarin da ya kai ga asarar rayuka da dukiyar al’umma.
Tinubu dai ya bukaci masu zanga-zangar da su janye tare da bude kofar yin zama domin tattaunawa.
Yanzu haka dai al’amura na kara ta’azzara a wasu jihohi kamar Filato, Kaduna da kuma Bauchi, inda jihohin suka sanya dokar hana fita a ranar Litinin.
A jihohin Kano, Yobe da Katsina kuwa, gwamnatocin jihohin sun sassauta dokar hana fitar ne duk da cewar ana ci gaba da gudanar zanga-zangar.
PDP ta ce abin da Tinubu da jami’yyarsa ke nuna wa ‘yan Nijeriya alama ce ta cewar kasar ba a gabansu ta ke ba.