Shugaba Bola Tinubu ya yi taron gaggawa da manyan sarakunan gargajiya a gidan Gwamnati (Aso Rock Villa) da ke Abuja ranar Alhamis.
Tawagar manyan sarakunan ta tawo ne a karkashin jagorancin Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar III da Ooni na Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi, Ojaja II.
- Wasu Ɓata-gari Na Iya Amfani Da Zanga-zanga Domin Tada Zaune Tsaye – Minista
- Tinubu Ya Gana Da Gwamnonin APC Kan Zanga-zangar Matsin Rayuwa
An fara taron ne da misalin karfe 2:30 na rana lokacin da shugaba Tinubu ya isa zauren majalisar. Duk da cewa, ba a bayyana musabbabin taron ba a lokacin tattaunawa da manema labarai, amma ana kyautata tsammanin cewa, ba zai rasa nasaba da shirin zanga-zanga a fadin kasar baki daya ba kan matsalar tabarbarewar tattalin arziki a ranakun 1 – 10 ga Agusta, 2024.
Manyan jami’an da suka halarci taron na Aso Rock, sun hada da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima; Sakataren gwamnatin tarayya, George Akume; Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, da babban sufeton ‘yansanda, Kayode Egbetokun.
Shugaban kungiyar gwamnonin Nijeriya (NGF), Gwamna Abdulrazaq Abdulrahman na jihar Kwara; Shugaban majalisar gwamnonin (PGF), Hope Uzodinma na jihar Imo; Ministan Kudi kuma Ministan Tattalin Arziki, Wale Edun, da Ministan Kasafin Kudi da Tsare Tattalin Arziki, Atiku Bagudu, duk sun samu halartar taron.
Kafin ganawar dai, shugaba Tinubu ya tattauna da gwamnonin APC a fadar shugaban kasa, duk da cewa, gwamnonin ba su yi wa manema labarai karin haske ba bayan ganawar tasu.