Biyo bayan tirjiya na karin kudin wutan lantarki da hukumomi suka yi a Nijeriya a watan da ta gabata, kungiyar kwadago a Nijeriya sun dukufa wajen gudanar da zanga-zanga tare da neman dole a canye zancen karin kudin wuta da kuma magance matsalar wutar lantarki.
Rahotonni sun yi nuni da cewa kungiyar kwadago sun rufe dukkanin ofisoshin kamfanonin rarraba wutar lantaki guda 11 da babban ofishin hukumar kula da wutar lantarki ta kasa a yayin da suka tsunduma gudanar da zanga-zangar na ranar Litinin.
- Sin: Karbuwar Hajojin Sin Masu Nasaba Da Sabbin Makamashi Ba Shi Da Nasaba Da Samar Da Tallafi
- Za A Bude Shafin Karbar Bashin Dalibai A Ranar 24 Ga Mayu
Shugaban kungiyar kwadago, Joe Ajaero shi ne ya jagoranci zanga-zangar a Abuja har zuwa ga ministan wuta da kuma shalkwatar hukumar kula da lamarin wuta a Nijeriya (NERC).
 Sannan an rufe ofishin kamfanin rarraba wutar lantarki tare da hana ma’aikata shiga domin gudanar da aiki.
 Bugu da kari, haka zancen yake a sauran ofisoshin kamfanin da ke jihohi da suka hada da na Kwara, Legas, Kaduna, Filato, Inugu, Sakkwato, Bauchi da sauran ofisoshi da suke sassan kasar nan.
Ajaero, yayin zanga-zangar, ya ce akwai bukatar NERC ta sake nazarin matakan da suka bi wajen karin kudin wuta. Ya ce, karin kudin ya janyo tashin farashin ababe da dama musamman kayan abinci.
 A martaninta kan zanga-zangar na kwana guda, gwamnatin Nijeriya ta ce ta fara tattaunawa da kungiyar kwadago kan lamarin.
Kakakin ministan wuta a Nijeriya, Florence Eke, ta shaida wa majiyarmu ta wayar tarho cewa bayan zanga-zangar ma’aikatan, gwamnatin tarayya ta hannun babban sakatare, Mista Mamman Mahmuda, ya kira taron ganawa da kungiyar kwadago a mako mai zuwa, ganawar da zai hada har da masu ruwa da tsaki domin lalubo bakin zaren matsalar.
“Ma’aikatar wuta za ta gayyaci dukkanin masu ruwa da tsaki domin nemo mafita kan wannan batun a mako mai zuwa,” ta shaida.
Mai magana da yawun kungiyar kwadago, Benson Upah, ya ce, ya kamata ne gwamnati ta tuntubi masu ruwa da tsaki tun kafin ta aiwatar da manufar karin kudin wutar a ranar 3 ga watan Afrilu.
Ya tabbatar da cewa zanga-zanga da suka fara muddin gwamnati ta kasa komawa baya kan matakinta na karin kudin lantarki za su ci gaba.
Idan za a tuna dai a watan Afrilun 2024 ne hukumar kula da wutar lantarki a Nijeriya ta sanar da karin kudin lantarki da kaso 240 ga kwastomomin da ke amfani da rukunin A.