Kungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF), na fargabar yadda matsalolin tsaro ke karuwa a kasar nan, yayin da matasa ke shirin gudanar da zanga-zanga kan rashin kyakkyawan shugabanci.Â
A taron da shugaban NGF kuma gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ya jagoranta, sun tattauna matsaloli da dama.
- Da Mu Za A Yi Zanga-zangar Matsin Rayuwa – NLC
- Zanga-zanga: Bauchi Ta Yi Hannun Riga Da Ikirarin Rufe Asibitoci
Mai bai wa shugaban kasa shawara kan sha’anin tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribadu, ya yi wa gwamnonin jawabi kan halin da ake ciki, inda ya bayyana cewa akwai bukatar daukar matakin gwamnati da gaggawa don dakile matsalolin tsaro yayin Zanga-zangar.
Ribadu ya yi alkawarin taimaka wa gwamnonin wajen inganta tsaro a matakin jihohi.
Manyan lauyoyin jihohi 36 sun yi magana kan hukuncin kotun koli game da ‘yancin cin gashin kai na kananan hukumomi.
Kungiyar lauyoyin Nijeriya (NBA) ta yi magana kan sauye-sauyen shugabanci da suka yi kwanan nan da kuma burinsu na yin aiki tare da jihohi don kare dimokuradiyya da bin doka.
Ministan lafiya, Farfesa Ali Pate, ya yi wa gwamnonin bayani kan ci gaban ayyukan kiwon lafiya karkashin shirin zuba jari na Sabunta bangaren kiwon lafiya na Nijeriya (NHSRIP).
Gwamnonin sun yi alkawarin ci gaba da aiki don inganta kiwon lafiya ga ‘yan Nijeriya.
Haka kuma, Mista Ndiame Diop, sabon daraktan kasashen duniya na Bankin Duniya, ya gabatar da shirye-shiryen HOPE da SPIN, wadanda ke da nufin inganta inganta tattalin arzikn jihohi.
Gwamnonin sun bayyana goyon bayansu ga wadannan shirye-shiryen.