• English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Zanga-zangar Minna: Shugaba Tinubu Ya Ba Da Umarnin A Sassauta Farashin Kayan Abinci – Idris

bySulaiman
2 years ago
Amurka

Zanga-zangar da mata suka gudanar a Minna, babban birnin Jihar Neja, dangane da tsadar kayan abinci da kuma tsadar rayuwa baki ɗaya, ta zaburar da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu har ya ba da umarni ga hukumomin da abin ya shafa da su gaggauta daƙile hauhawar farashin kayan abinci a faɗin ƙasar nan.

Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da da Kai, Alhaji Mohammed Idris ne ya bayyana hakan Jim kadan bayan tashi daga taron da Kwamitin Shugaban Ƙasa kan bada Agajin gaggawa na raba abinci ya yi a ranar Talata a Abuja.

  • An Hada Rukunin Karshe Na Tashar Samar Da Wutar Lantarki Da Sin Ta Gina A Uganda Da Layin Wutar Lantarki Na Kasa
  • Gwamnan Zamfara Ya Kaddamar Da Kwamitin Asusun Samar Da Tallafin Tsaro

Idris ya ce Shugaban Ƙasa ya damu sosai dangane da yadda abinci ke ƙara tsadar nesanta kan sa daga talakawa a faɗin ƙasar nan.

Ministan ya ce, zanga-zangar da mata suka yi a Minna dangane da tsadar abinci, ya zaburar da Gwamnatin kan ɗaukar wasu matakai domin tabbatar da cewa ‘yan Nijeriya sun samu sauƙi da rahusa, ta yadda abinci ba zai riƙa neman gagarar su ba.

Ya ƙara da cewa kwamitin zai ci gaba da yin taro har zuwa ranar Alhamis.

LABARAI MASU NASABA

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

Ya ce tuni aka fara ɗaukar wasu muhimman matakai domin rage wa jama’a raɗaɗin tsadar rayuwa da tsadar farashin kayan abinci.

Ya ce: “Daga cikin matakan akwai gaggauta fito da kayan abincin da gwamnatin tarayya ta tanadar a rumbunan ajiyar abincin gwamnati da ke faɗin ƙasar nan.

“Sannan kuma gwamnati na tattaunawa da manyan masu sarrafawa ko cashe kayan abinci da manyan ‘yan kasuwar kayan abinci da kayan masarufi, domin tantance adadin abin da suke da shi a ajiye a rumbunan ajiyar su.

“Dalilin yin hakan shi ne gwamnati na so ta gaggauta shiga cikin lamarin domin abinci ya wadata ga ‘yan Nijeriya.”

Sai dai kuma ya yi tsokacin cewa, gwamnati na sane akwai wasu marasa kishin kasa kuma marasa tausayi da ke ɓoye abinci domin su sayar idan ya yi tsada sosai.

“Gwamnati ba za ta zura ido ‘yan Nijeriya na fama da tsadar kayan abinci ba, alhali wasu na haifar da ƙarancin sa. Don haka ina roƙon jama’a su fahimci irin damuwar gwamnati da kuma ƙoƙarin da ta ke yi.

“Yayin da aka kammala waɗannan tarukan, za mu fito da sanarwa dangane da matsayi da matakan da gwamnati ta ɗauka.”

Taron ya samu halartar Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila; Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Yemi Cardoso; Ministan Harkokin Kuɗaɗe, Wale Edun, da Mashawarcin Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu.

Sauran sun haɗa da Ministan Noma, Abubakar Kyari, na Kasafin Kuɗaɗe Da Tsare-tsare, Atiku Bagudu, sai kuma Ƙananan Ministocin Gona da FCT Abuja, Sabi Abdullahi da Mariya Mahmood.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

A Kama Wani Likitan Bogi A Neja
Labarai

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno
Labarai

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio
Manyan Labarai

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Next Post
Yadda Nijeriya Ta Taka Rawar Gani Har Zuwa Zagayen Karshe Na Gasar AFCON

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

October 7, 2025
Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

October 7, 2025
Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version