Bayan isowar Gwamna Abba Yusuf daga Abuja a ranar Talata tare da wasu kananan yara 63 da aka yi wa afuwa da aka kama tare da tsare su a yayin gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa a watan Agusta a Kano, gwamnan ya ce, yaran za su kwashe kimanin kwanaki biyar a Asibiti domin kula da lafiyarsu.
An kai masu zanga-zangar da aka yi wa afuwa wadanda galibinsu kananan yara ne kai tsaye asibitin kwararru na Muhammadu Buhari da ke cikin birnin Kano, inda za a kula da lafiyarsu.
- Yaya Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Ya Jagoraci Zamanantarwar Kasashe Masu Tasowa?
- Da Ɗumi-ɗumi: DisCos Ya Sanar Da Sabbin Farashin Mitar Wutar Lantarki
Gwamna Yusuf ya bayyana hakan ne a wani liyafa ta musamman da aka yi wa yaran a asibitin a daren ranar Talata.
Gwamna Yusuf ya kara da cewa, zai dauki nauyin karatun yaran a karkashin ma’aikatar ilimi inda kwamishinan da tawagarsa za su ziyarci asibitin domin tantance matakin karatun da suke a halin yanzu.
Ga waɗanda ba su zuwa makaranta, za a taimaka musu da sana’o’in fasaha tare da ba su kayan aiki don fara kasuwanci.