Rundunar ‘Yansandan Nijeriya, ta nemi ƙungiyar Amnesty International ta janye wani rubutu da ta wallafa mai zargin jami’an ‘yansanda da cin zarafin masu zanga-zangar tsadar rayuwa da aka gudanar a watan Agustan 2024.
A sanarwar da kakakin ‘yansandan, ACP Muyiwa Adejobi, ya fitar, an bayyana cewa rubutun Amnesty ya caccaki jami’an ‘yan sanda da zargin amfani da karfi fiye da ƙima da kuma tauye haƙƙin bil adama.
- Abubuwan Dake Kunshe Cikin Rahoton Shekara-Shekara Game Da Cinikin Shige Da Fice Na Kasar Sin
- Bafarawa Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP
Amma rundunar ta musanta dukkanin zarge-zargen a matsayin marasa tushe.
Rundunar ta buƙaci Amnesty ta janye rubutun tare da neman afuwa a bainar jama’a cikin kwanaki bakwai, idan ba haka ba za ta ɗauki matakin shari’a don kare mutuncinta.