‘Yan kwanaki kalilan ya rage a bude taron jagororin kungiyar BRICS karo na 15. Game da hakan, yayin wata zantawa da manema labarai, Dilma Rousseff, shugabar sabon bankin samar da ci gaba, kuma tsohuwar shugabar kasar Brazil, ta ce bankin da take jagoranta yana kan hanyar bunkasa, kuma yana da burin samar da kudade ga kasashe masu tasowa, don gudanar da manyan ayyukan sauya alkibla, wadanda za su zaburar da matakan bunkasa cudanyar sassan duniya daban daban.
Dilma Rousseff na ganin cewa, gogewar da ta samu a matsayin ta na tsohuwar shugabar kasa, ya ba ta damar gudanar da jagoranci bisa kwarewa.
A cewar ta, tsarin hadin gwiwar BRICS zai taka rawar gani, wajen bunkasa wanzuwar zaman lafiya da ci gaban duniya. Daga nan sai ta bayyana adawar ta ga takunkumai, da mayar da hada hadar kudade wani makami na cimma burin kashin kai, tana mai ganin baiken babakeren dalar Amurka, tare da ba da shawarar amfani da kudaden kasashe daban daban yayin da ake raya harkokin cinikayya.
Dilma Rousseff, ta kuma jinjinawa salon yaki da fatara na kasar Sin, tana mai fatan ziyarar biranen Shenzhen da Yan ‘an, kana ta ce abubuwan da suka auku a kasar Sin, za su yi tasiri matuka ga ci gaban daukacin rayuwar bil’ adama. (Saminu Alhassan)