Kotun shari’ar Musulunci da ke kwana hudu, ta umarci a mika Murja Kunya Asibitin ƙwaƙwalwa domin duba lafiyarta saboda irin dabi’un da ta nuna yayin zaman kotun da akayi a safiyar yau Talata don ci gaba da sauraron shari’ar zarge-zargen da ake yi mata.
Mai Shari’a Mallam Nura Yusuf Ahmad ne ya bawa Hukumar Hisbah umarnin kai Murja wajen likitan ƙwaƙwalwa domin duba lafiyarta sai ranar 20 ga watan Mayun 2024 za’a dawo don nuna wa Kotu sakamakon binciken da likitan ya yi.
- Dambarwar Shari’ar Murja Kunya: Gwamnatin Kano Ta Musanta Yin Katsalandan Kan Shari’ar
- ‘Yan Kasuwar Kano Sun Nemi Gwamnati Ta Kawo Dauki Kan Halin Da Kasuwannin Ke Ciki
Tun da farko dai, hukumar Hisbah ce ta shigar da kara tana tuhumar Murja Kunya da yada badala da ta saba da addini da al’adar mutanen Kano.
In ba a manta ba, mun rahoto muku dambarwar da ta kaure bayan da aka nemi Murja a gidan gyara hali aka rasa, inda Mutane da dama suka yi zargin cewa, Gwamnatin Kano ta yi katsalandan kan tuhumar da ake yi wa Murja amma Gwamnatin ta musanta zargin da cewa, Jami’an tsaro ne suka fitar da ita kan wata tuhuma da suke yi mata.