Hukumar yaki da aikata rashawa da dangoginta (ICPC) ta cafke wani dan kwangilar kotun koli, Temitope Banjoko bisa zargin badakalar kudade da kuma kwangilar bogi.
Majiyoyi daga ICPC sun tabbatar cafkewa da tsare Banjoko, manajan daraktan kamfanin Asbat construction limited wa LEADERSHIP ta wayar tarho cewa, kamfanin an zarge shi da karban aikin kwangilar da ya kai naira N46,305,000 (N41,674,500 bayan cire haraji) domin rushewa da kwashe rusheshshen ginin gidaje guda hudu a matsunin gidajen Alkalai da ke Maitama, Abuja a shekarar 2017.
Majiyoyin sun ce aikin da aka bayar din ba a gudanar da shi ba duk kuwa da cewa an biya cikakken kudin aikin ga kamfanin Asbat, wanda a bisa hakan ne ya sanya ICPC ta kaddamar da bincike.
Majiyoyin sun ce, a lokacin da ake masa tambayoyi, dan kwangilar ya yi ikirarin cewa, ya yi amfani da kudaden ta wasu hanyoyin daban tare da nuna fargabar cewa kudaden ba zai yiyu su dawo ba, wanda hakan ya saba wa doka.
Kazalika, mamallakin kamfanin, Banjoko an ce ya yi alkawarin dawo da kudaden da fari da ICPC ta fara bincike, amma daga cikin kudaden kwangilar naira miliyan biyar kacal ya iya dawo da shi, tare da sauran N36,674,500 da suka bace bat.
Majiyoyin sun kuma ce, binciken da ICPC ta gudanar ya iya gano mata cewa wasu daga cikin gidajen da aka bada kwangilar yanzu haka ma an musu kwaskwarima har ma wasu alkalan suna ciki. Hakan na nuni da cewa aniyar rushe gidajen babu shi gaba daya sai dan an cire kudin da aka ware da sunan rushe gidajen kuma kudaden sun gaza dawowa.
Ana sa ran ICPC za ta gurfanar da kwangilar a kotu a ‘yan kwanaki masu zuwa.