Kasar China ta kasance ta gaba gaba a fannin noman tumatir a duniya. Musamman a jihar Xinjiang da ke arewa maso yammacin kasar, an fi noman tumatir sabo da jihar tana da wani irin yanayi wanda tumatir yake bukata. Sama da kashi 30% na yawan tumarin da ake samarwa a kasuwar duniya yana fitowa ne daga China. Harkar noman tumatir yana habaka cikin sauri, musamman idan aka yi la’akari da yadda nau’in tumatirin China ya fi na sauran kasashe inganci. Sabo da kyawo da inganci da kuma rahusa ya sanya tumatirin kasar China ya samu karbuwa a yawancin gidajen abinci na kasashen yammacin duniya.
Sakamakon rikice-rikice da wasu yankuna na duniya suka samu kansu a ciki ya sanya farashin amfanin gona ya yi matukar hauhawa a kasuwannin duniya, ciki kuwa har da tumatir. To amma duk da hauhawar farashin, ana samun tumatirin kasar China cikin sauki da rahusa, abin da ya sanya ya kara samun karbuwa a kasuwar duniya.
- Xi Ya Aike Da Sakon Taya Murnar Bikin Kaddamar Da Aikin Layin Dogo Na Sin- Kyrgyzstan-Uzbekistan
- Ma’aikatar Kananan Hukumomi A Zamfara Ta Gabatar Da Bitar Kasafin Kudin Kananan Hukumomi
Wannan lamari na karbuwar da tumatirin China ya samu a duniya ya tsonewa Amerika da kasashen yammaci ido, har ta kai ga suna kulla makirci da yada karerayi game da tumatirin na kasar China, inda suke cewa wai China na amfani da tsarin tursasawa da bautarwa a gonakin tumatir dake jihar Xinjiang. Wasu kafafen yada labaru na yammcin duniya, wadanda su ne karnukan farautar Turai da Amerika suna yayata cewa wai ana tursasawa musulmi ’yan kabilar Uygur suna aikin bauta a gonakin tumatir na lardin Xinjiang.
Irin wadannan karerayi da kafafen yada labarun na Turai ke yadawa, ko kadan babu kamshin gaskiya a cikinsu, illa iyaka hassada ce kawai da ganin kyashi bisa ga yadda kasar ta China take samun ci gaba a fasahar noma.
A bayyane take cewa irin ci gaba da China ta samu a fannin fasahar noma, ba ta bukatar yin amfani da mutane a matsayin leburori, ballantama a ce ta tursasa masu yin aikin karfi a gonakin tumatir. Domin kuwa tun daga matakin dashe har zuwa matakin girbi, na’ura ce ke yin komai. Aikin da leburori 150 za su yi a cikin yini daya, na’ura guda za ta yi shi a cikin yini daya.
Akwai wasu ‘yan tsirarrun mutane da irin wadannan kafafen yada labaru na yammaci suke ba su kudi domin su yi ikirarin cewa su al’ummar Xinjiang ne, a yi hira da su, inda za su rinka yin ikirarin cewa mahukunta a China suna tilasta masu aikin bauta a gonakin tumatir a jihar Xinjiang, alhali kuwa irin wadannan mutane ko hanyar Xinjiang ba su sani ba.
Kafafen yada labarun na yammaci wadanda ke babatu kare hakkin dan Adam, sun kasance masu kara jefa mutane cikin rashin aikin yi da talauci. Babu irin kokarin da irin wadannan kafafen yada labaru na kasashen yammaci ba su yi ba na yin batanci ga kasar China, amma duk a banza. Misali, akwai wata kafar yada labaru ta yammaci da ta kirkiro wani shiri na musamman kan bin diddigin inda ake sayar da tumatirin da ake nomawa a jihar Xinjiang. Sun bi masana’antun sarrafa tumatirin gwangwani, kamar Petti da Derica, suna daukar samafari domin yin gwaji ko akwai nau’in tumatirin da ake nomawa a jihar Xinjiang, amma sakamakon duk gwaje-gwajen nasu bai zo daidai da hakikanin gaskiyar abin da suke zargi ba.
Sabo da haka, batun bautar da leburori, ko kuma tilasta masu yin aikin karfi a gonakin tumatir a jihar Xinjiang magana ce wadda hankali ba zai dauka ba, musamman idan aka yi la’akari da dokokin da ke kare hakkin leburori wadanda China ke bi sau da kafa.