Cikin manyan batutuwa da sakatariyar baitil-malin Amurka Janet Yellen ta tabo, yayin ziyarar kwana kwanan nan da ta yi a kasar Sin, akwai zargin Sin da “Wuce Misali” a fannin bunkasa masana’antu masu alaka da makamashi mai tsafta, ciki har da na samar da ababen hawa masu aiki da lantarki.
Kafin ziyarar Yellen, kafafen watsa labaran Amurka sun yi ta yayata batun nan na “Wuce Misali” a fannin kere keren kasar Sin, suna zargin Sin din da cika kasuwannin duniya da kayayyakin fitarwa ketare masu rahusa, irin su farantan samar da lantarki ta hasken rana da ababen hawa masu aiki da lantarki.
- Xi Ya Aike Da Sakon Ta’aziyya Ga Shugaban Kasar Mozambique
- Firaministan Kasar Sin Ya Jagoranci Taron Neman Ra’ayi Kan Aikin Tattalin Arziki
To sai dai kuma, wadannan zarge-zarge ba su da tushe ko makama. Suna kuma fayyacewa duniya halayyar masu tsara manufofi na Amurka, dake da tunanin ko kasar su ta samu, ko kuma kowa ya rasa.
Karkashin irin wannan tunani ne mahukuntan Amurka suka kakaba takunkumin hana fitar da sassan laturori na kamfanonin kasar zuwa kasuwannin Sin, da hana wasu kamfanonin Sin din damar kasuwanci na halak ta fakewa da tsaron kasa.
Har ila yau, irin wadannan matakai na nuni ga matsayin Amurka na aiwatar da manufofi idan kawai za su yi daidai da moriyar kasar, da saba musu idan za su amfani sauran sassa. Wato dai a duk lokacin da masana’antun Amurka za su ci wata gajiya, kasar na yin “Uwa da makarbiya” wajen ganin sun cimma nasara, amma idan kamfanonin kasar za su yi takara da na sauran sassan duniya, sai Amurkan ta sanya shinge na baiwa kamfanoninta kariya, wanda hakan sam ya sabawa adalci.
A gani na, maimakon zargin “Wuce Misali” kan kamfanoni masu alaka da makamashi mai tsafta na Sin, kamata ya yi ma Amurka da sauran kasashen duniya su goyi bayan ci gaban wannan fasahohi, duba da cewa a yanzu haka ana kan wata gaba da kasashen duniya ke ta kokarin sauya alkibla zuwa amfani da nau’o’in makamashi marasa gurbatawa da dumama yanayi.
A daya bangaren kuma, mun san cewa Sin da Amurka kasashe ne dake da bangarori da dama na hadin gwiwa da cin moriyar juna. Don haka ne ma har kullum, mahukuntan kasar Sin ke ganin abun da ya fi dacewa shi ne sassan biyu su ingiza ci gaban juna maimakon takawa juna birki, a dukkanin bangarori na ci gaba da aka saba da su na cinikayya, da noma, da ma sabbin fannoni irin su na kare yanayi, da fasahohi, da ayyukan kirkirarriyar basira ko AI.