• English
  • Business News
Monday, November 3, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Zargin Tarkon Bashi Ba Zai Katse Alakar Sin Da Kasashen Afirka Ba

by CMG Hausa
3 years ago
Alakar Sin da Afirka

Sau da yawa mun sha jin yadda wasu kasashen yammacin duniya, da kafofin watsa labaransu na furta kalamai na zargi, cewa wai kasar Sin tana danawa kasashen dake nahiyar Afirka Tarko Bashi, karkashin manufofinta na cudanyar da kasashe masu tasowa.

Irin wadannan sassan, kan Ambato shawarar ziri daya da hanya daya, a matsayin shiri dake dorawa kasashen na Afirka tarin bashi da ba za su iya biya ba. To amma abun tambayar shi ne, ko kasashen na Afirka suna da irin wannan tunani?

  • Jarin Waje Da Sin Ta Yi Amfani A Zahiri Ya Karu A Shekarar 2022

A zahiri dai, ba wata kafa da ta taba fito da shaidu, ko kafa sahihan dalilai kan wancan zargi da wasu kasashen yamma ke yiwa kasar Sin. Hasali ma, sau da yawa mun sha jin shugabannin kasashen Afirka na godewa irin tallafi, da gudummawar da Sin din ke ba su, a kokarinsu na raya kasa da samun ci gaba mai dorewa.

Ko da a yayin ziyarar aiki da ministan harkokin wajen kasar Sin Qing Gang ya kai kasashen Afirka 5, da helkwatar AU, da kungiyar tarayyar Larabawa a baya bayan nan, mun ga irin yadda bangarorin da ya zanta da su suka rika nuna gamsuwa, da godiya kan manufofin kasar Sin, na tafiya tare da kawayenta na Afirka, a matsayinsu na aminai, kuma ’yan uwan ta kasashe masu tasowa.

Kaza lika, masana tattalin arziki da dama na bayyana cewa, bashin da gwamnatoci ke karba daga waje, ba ya haifar da koma bayan tattalin arziki, muddin an aiwatar da sharudda, da matakan cin gajiyarsa yadda ya kamata. Kuma karkashin hakan ne ragowar cibiyoyin bayar da lamuni na yammacin duniya, suke baiwa kasashen na Afirka lamuni mai kudin ruwa, tare da gindaya sharudda gare su na biyan basussukan. Sabanin haka, kasar Sin a nata bangare, ba ta gindaya sharudda ga kasashen da take baiwa bashi, kuma bashin Sin yana da rangwame matuka, idan an kwatanta da na sauran cibiyoyin ba da lamuni na kasa da kasa.

LABARAI MASU NASABA

Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murnar Bude Babban Gidan Tarihi Na Kasar Masar

Ziyarar Shugaba Xi A Koriya Ta Kudu Ta Bude Babin Yaukaka Hadin Gwiwar Yankin Asiya Da Fasifik

Idan kuma muka komawa misalai daga su kansu jagororin kasashen Afirka, da kuma alkaluman da hukumomin nahiyar ke fitarwa, game da tasirin lamunin kasar Sin a nahiyar Afirka, za mu ga a kasashe irin su Najeriya, da Zambia, da Kenya da Angola da sauransu, ayyukan more rayuwa da kasar Sin ta tallafawa wajen samarwa, suna zamewa kasashen abubuwan alfahari.

Duba da haka, masharhanta da dama ke cewa, su kansu kasashen yamma, da masana na kasashen yammacin duniya, sun gamsu da kyakkyawan tasirin alakar Sin da kasashen Afirka, da ma yadda Sin din ke samar da tallafi ga ci gaban tattalin arziki da zamantakewar alummun nahiyar. Amma duk da haka, wasu bangarori na kitsa karairayi, domin bata wannan kyakkyawar alaka, ta fakewa ba batun “Tarkon bashi “. Suna kuma yada kalamai marasa hujja, da nufin siyasantar da alakar dake tsakanin sassan biyu.

Sai dai duk da haka, alamu na zahiri sun tabbatar da cewa, Sin da kasashen Afirka sun amince da juna, kuma ba wani rukuni, ko wasu masu kitsa karairayi da za su iya yin nasarar bata wannan kyakkyawar alakar da sassan biyu suka gina cikin tsawon lokaci. (Saminu Hassan)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murnar Bude Babban Gidan Tarihi Na Kasar Masar
Daga Birnin Sin

Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murnar Bude Babban Gidan Tarihi Na Kasar Masar

November 2, 2025
Ziyarar Shugaba Xi A Koriya Ta Kudu Ta Bude Babin Yaukaka Hadin Gwiwar Yankin Asiya Da Fasifik
Daga Birnin Sin

Ziyarar Shugaba Xi A Koriya Ta Kudu Ta Bude Babin Yaukaka Hadin Gwiwar Yankin Asiya Da Fasifik

November 2, 2025
Taron APEC Na 2026 Da Za A Shirya A Kasar Sin Zai Bude Sabon Babin Na Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik
Daga Birnin Sin

Taron APEC Na 2026 Da Za A Shirya A Kasar Sin Zai Bude Sabon Babin Na Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik

November 2, 2025
Next Post
Na Sake Dawowa Musulunci, Cewar JJC Skills

Na Sake Dawowa Musulunci, Cewar JJC Skills

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Kashe Ƴan Bindiga 19, Sun Ƙwato Makamai A Kano

Sojoji Sun Kashe Ƴan Bindiga 19, Sun Ƙwato Makamai A Kano

November 3, 2025
Zamfara Ta Tashi Daga Matsayi Na 36 Zuwa Na 17 A Shekara Biyu Ƙarƙashin Gwamna Lawal — Rahoton BudgIT

Zamfara Ta Tashi Daga Matsayi Na 36 Zuwa Na 17 A Shekara Biyu Ƙarƙashin Gwamna Lawal — Rahoton BudgIT

November 3, 2025
Sabon Muƙaddashin Shugaban PDP Ya Sha Alwashin Maido Da Martabar Jam’iyyar Kafin 2027

Sabon Muƙaddashin Shugaban PDP Ya Sha Alwashin Maido Da Martabar Jam’iyyar Kafin 2027

November 3, 2025
2023: Gwarazan Jam’iyyu A Karon Battar Zaben Shugaban Kasa

Mayar Da Martani Kan Barazanar Amurka Ga Nijeriya: Fadar Shugaban Ƙasa Ta Yaba Wa Kwankwaso 

November 3, 2025
Likitoci

NARD Ta Yi Fatali Da Iƙirarin Gwamnatin Tarayya Na Ba Ta ₦43bn, Kuma Yajin Aiki Na Nan

November 3, 2025
Kano

Kano Ta Amince Da Naira Biliyan 8.2 Don Ayyukan ilimi, Samar Da Ruwa, Da Makamashi

November 3, 2025
Kwankwaso Ya Gargaɗi Trump Kan Barazana Ga Nijeriya

Kwankwaso Ya Gargaɗi Trump Kan Barazana Ga Nijeriya

November 2, 2025
Gumi Ya Nemi Nijeriya Ta Katse Hulɗa Da Amurka Idan Trump Bai Janye Barazanar Sa Ba

Gumi Ya Nemi Nijeriya Ta Katse Hulɗa Da Amurka Idan Trump Bai Janye Barazanar Sa Ba

November 2, 2025
Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murnar Bude Babban Gidan Tarihi Na Kasar Masar

Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murnar Bude Babban Gidan Tarihi Na Kasar Masar

November 2, 2025
Ƙasashen Da Ba Su Yanke Hukuncin Kisa A Duniya Ba

Ƙasashen Da Ba Su Yanke Hukuncin Kisa A Duniya Ba

November 2, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.