Cibiyar Daƙile Cututtuka ta Nijeriya (NCDC), ta tabbatar da mutuwar mutane 22 tare da samun ƙarin mutane 143 da suka kamu da cutar zazzabin Lassa cikin makonni biyun farko na shekarar 2025.
A mako na biyu, adadin masu cutar ya ƙaru daga mutane 54 a mako na farko zuwa mutand 89.
- Yajin Aikin Likitoci Ya Tsayar Da Al’amura A Asibitocin Abuja
- Sabon Albishir Ga Masu Kawo Ziyara Ko Yada Zango A Birnin Beijing Na Kasar Sin
An fi samun rahotannin waɗanda suka kamu da cutar a jihohin Ondo, Edo, da Bauchi, waɗanda suka haura kashi 77 na dukkanin adadin.
Cutar ta fi shafar mutane masu shekaru tsakanin uku zuwa 78.
NCDC ta bayyana cewa adadin waɗanda suka rasu ya ragu zuwa kashi 15.4 idan aka kwatanta da kashi 16.4 na shekarar 2024.
Amma ta yi gargaɗin cewa yanayin na da matuƙar muhimmanci.
An ƙaddamar da tsarin gaggawa don ƙarfafa matakan daƙile cutar.
Haka kuma, cibiyar ta shawarci ‘yan Nijeriya su kula da tsaftar abinci, hana ɓeraye shiga gidaje, da gaggauta neman magani idan sun ga alamun zazzaɓin ko jini.