• English
  • Business News
Monday, November 10, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Zhang Jun: Sin Za Ta Ci Gaba Da Taka Rawar Gani Wajen Cimma Burin Bunkasa Afirka Cikin Lumana

by CGTN Hausa
2 years ago
Zhang Jun

Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Zhang Jun ya ce, kasarsa za ta ci gaba da taka rawar gani, a fannin ingiza bunkasar nahiyar Afirka cikin lumana, tare da fadada hadin gwiwar nahiyar da sauran sassan kasa da kasa.

Zhang, wanda ya bayyana hakan a jiya Alhamis, ya kuma yi amfani da zaman taron kwamitin tsaron MDD da ya gudana a ranar, mai taken “Hadin gwiwa tsakanin MDD da kungiyar AU” wajen bayyana cewa, a shekarun baya bayan nan, kungiyar AU da sauran hukumomin yankin Afirka, na aiki tukuru wajen tunkarar kalubalen zaman lafiya da tsaro, suna kuma kokarin ingiza matakan warware matsalolin nahiyar.

  • Kudaden Da Sin Ta Samarwa Kasashen Afirka Ba Su Kai 10% Na Bashinsu Ba
  • Xi Ya Yi Kira Ga Jiangxi Da Ya Rubuta Nasa Babin A Kokarin Zamanantar Da Kasar Sin

Ya ce yayin da ake tunkarar kalubale daban daban a sassan duniya da yankuna, kamata ya yi kwamitin tsaron MDD ya ci gaba da tallafawa AU, wajen karfafa wannan yunkuri. Kaza lika ya dace tawagogin wanzar da zaman lafiya na MDD su rungumi dabarun da AU ke amfani da su, kana su amince da sauye-sauyen yanayin da ake ciki, su kuma sauke nauyin dake wuyan su yadda ya kamata.

Zhang Jun ya kara da cewa, a halin da ake ciki, yankin kahon Afirka na fuskantar manyan matsaloli masu sarkakiyar warwarewa, kana ana fama da yanayin rashin tabbas a siyasar kasashen yammacin Afirka da Sahel, ga kuma kalubalen ’yan ta’adda dake haifar da tashin hankula, a babban yankin tafkin Chadi. Ya ce wadannan batutuwa ne masu matukar haifar da damuwa. Don haka ya dace MDD ta tallafawa nahiyar Afirka, wajen cimma nasarar muradun dake kunshe cikin ajandar wanzar da ci gaba mai dorewa ta nan da shekarar 2030, kana ta kara azama wajen tallafawa yaki da talauci, da tabbatar da samuwar isasshen abinci, da karfafa samar da muhimman ababen more rayuwa, da fadada samar da guraben ayyukan yi.

Daga nan sai Zhang Jun ya jaddada matsayar kasar Sin, ta mara baya ga sanin makamar aiki tsakanin kasashen nahiyar Afirka, a matsayin daya daga muhimman ginshikai na hadin gwiwa da nahiyar, baya ga burin da Sin din ke da shi na taimakawa nahiyar a fannin bunkasa masana’antu, da zamanantarwa, da wanzar da ci gaba. (Mai fassara: Saminu Alhassan)

LABARAI MASU NASABA

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Ci Gaba Da Zama Muhimmin Ginshiki Ga Ci Gaban Nahiyar 

An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Ci Gaba Da Zama Muhimmin Ginshiki Ga Ci Gaban Nahiyar 
Daga Birnin Sin

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Ci Gaba Da Zama Muhimmin Ginshiki Ga Ci Gaban Nahiyar 

November 9, 2025
An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025
Daga Birnin Sin

An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025

November 9, 2025
Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa
Daga Birnin Sin

Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa

November 9, 2025
Next Post
Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Da Su Yi Aiki Tare Don Hana Kara Fadada Rikicin Falasdinu Da Isra’ila

Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Da Su Yi Aiki Tare Don Hana Kara Fadada Rikicin Falasdinu Da Isra'ila

LABARAI MASU NASABA

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Ci Gaba Da Zama Muhimmin Ginshiki Ga Ci Gaban Nahiyar 

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Ci Gaba Da Zama Muhimmin Ginshiki Ga Ci Gaban Nahiyar 

November 9, 2025
An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025

An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025

November 9, 2025
Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL

Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL

November 9, 2025
Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa

Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa

November 9, 2025
CMG Ya Cimma Yarjejeniyar Samun Iznin Watsa Shirye-shiryen Wasannin Olympics Daga Shekarar 2026 Zuwa 2032

CMG Ya Cimma Yarjejeniyar Samun Iznin Watsa Shirye-shiryen Wasannin Olympics Daga Shekarar 2026 Zuwa 2032

November 9, 2025
Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Na Gwaji

Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Na Gwaji

November 9, 2025
Shugaba Xi Ya Ayyana Bude Gasar Wasanni Ta Kasa Karo Na 15

Shugaba Xi Ya Ayyana Bude Gasar Wasanni Ta Kasa Karo Na 15

November 9, 2025
Mizanin Farashin Kayan Masarufi Na Kasar Sin Ya Karu Da 0.2% A Watan Oktoba

Mizanin Farashin Kayan Masarufi Na Kasar Sin Ya Karu Da 0.2% A Watan Oktoba

November 9, 2025
Me Ke Haddasa Yawaitar Farmakar Ƴan Wasa A Gasar Firimiyar Nijeriya

Me Ke Haddasa Yawaitar Farmakar Ƴan Wasa A Gasar Firimiyar Nijeriya

November 9, 2025
NBA Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Hukuncin Alƙalai Ke Karo Da Juna

NBA Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Hukuncin Alƙalai Ke Karo Da Juna

November 9, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.