• English
  • Business News
Monday, July 28, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Zhang Jun Ya Soki Amurka Game Da Gazawarta Na Daidaita Batun Takunkuman Da Aka Kakabawa Sudan Ta kudu

by CMG Hausa
3 years ago
in Daga Birnin Sin
0
Zhang Jun Ya Soki Amurka Game Da Gazawarta Na Daidaita Batun Takunkuman Da Aka Kakabawa Sudan Ta kudu
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Zhang Jun ya soki kasar Amurka, bisa gazawarta na daidaita batun takunkuman da aka kakabawa kasar Sudan ta kudu.

Zhang Jun ya ce, Amurka ta gaza sauke nauyin dake wuyanta, a matsayinta na mai gabatar da kuduri a kwamitin tsaron MDD, kan batun dake da nasaba da takunkumai kan Sudan ta kudu.

Jami’in ya ce nauyi ne a wuyan kasa mai kujerar dindindin a kwamitin tsaro, ta gabatar da gamsasshen bayanin yadda za a cimma matsaya, maimakon kafewa kan nata ra’ayi na kashin kai.

Kasashe da dama mambobin kwamitin tsaron MDD, ciki har da na nahiyar Afirka, sun nuna rashin gamsuwa game da kudurin da aka gabatar.

To sai dai kuma Amurka ta ci gaba da nacewa, wajen tabbatar da matsayarta, game da kudurin da bai samu goyon bayan sauran sassa ba. Don haka ne ma, kasar Sin ta yanke shawarar kin jefa kuri’ar ta.

Labarai Masu Nasaba

Sin Ta Samar Da Manyan Manhajojin AI Sama Da 1500

Zhao Leji Ya Kai Ziyarar Sada Zumunta A Kyrgyzstan

Su ma kasashen Gabon, da India, da Kenya, da Rasha sun kauracewa kada kuri’unsu a kudurin na jiya Alhamis, wanda ke kunshe da sabunta kakabawa Sudan ta kudu takunkumi.

A jiya Alhamis ne kwamitin tsaron MDD ya amince da kuduri mai lamba 2633, wanda ya tanaji tsawaita takunkumin hana Sudan ta kudu sayen makamai, da sauran takunkuman da suka shafi kasar, har zuwa ranar 31 ga watan Mayun shekara mai zuwa. (Saminu)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Wang Yi Yayi Bayani Game Da Manufar Sin Kan Raya Dangantakar Dake Tsakaninta Da Kasashen Tekun Pasifik

Next Post

Sabuwar Manufar Amurka Kan Sin Ba Ta Canja Tunaninta Na Yakin Cacar Baka Da Fin Karfi Ba

Related

Sin Ta Samar Da Manyan Manhajojin AI Sama Da 1500
Daga Birnin Sin

Sin Ta Samar Da Manyan Manhajojin AI Sama Da 1500

41 minutes ago
Zhao Leji Ya Kai Ziyarar Sada Zumunta A Kyrgyzstan
Daga Birnin Sin

Zhao Leji Ya Kai Ziyarar Sada Zumunta A Kyrgyzstan

21 hours ago
Sin Ta Samu Ci Gaban Aikin Jigilar Kaya A Rabin Farko Na Bana
Daga Birnin Sin

Sin Ta Samu Ci Gaban Aikin Jigilar Kaya A Rabin Farko Na Bana

22 hours ago
Kudin Shigar Da Kasuwar Fina-Finai Ta Sin Ta Samu A Lokacin Zafi Na Bana Ya Zarce Yuan Biliyan 5
Daga Birnin Sin

Kudin Shigar Da Kasuwar Fina-Finai Ta Sin Ta Samu A Lokacin Zafi Na Bana Ya Zarce Yuan Biliyan 5

23 hours ago
Shanghai Ya Gabatar Da Shirin Gina Yankin Motoci Masu Tuka Kansu
Daga Birnin Sin

Shanghai Ya Gabatar Da Shirin Gina Yankin Motoci Masu Tuka Kansu

24 hours ago
Sin: Fasahar Rage Asarar Hatsi Ta Yi Amfani
Daga Birnin Sin

Sin: Fasahar Rage Asarar Hatsi Ta Yi Amfani

1 day ago
Next Post
Sabuwar Manufar Amurka Kan Sin Ba Ta Canja Tunaninta Na Yakin Cacar Baka Da Fin Karfi Ba

Sabuwar Manufar Amurka Kan Sin Ba Ta Canja Tunaninta Na Yakin Cacar Baka Da Fin Karfi Ba

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Samar Da Manyan Manhajojin AI Sama Da 1500

Sin Ta Samar Da Manyan Manhajojin AI Sama Da 1500

July 28, 2025
Kakakin Majalisar Wakilai, Abbas, Ya Yi Jimamin Rasuwar Buhari, Ya Ce Mutuwa Ce Da Ta Girgiza Shi

SDP: Fadar Shugaban Ƙasa Ta Yi Wa El-Rufai Shaguɓe Da Ayyana Shi A Matsayin Ɗan Gudun Hijirar Siyasa

July 28, 2025
Sojoji, DSS Sun Hallaka Ƴan Bindiga 45 A Neja

Sojoji, DSS Sun Hallaka Ƴan Bindiga 45 A Neja

July 28, 2025
SDP Ta Kori Tsohon Gwamnan Kaduna El-Rufai

SDP Ta Kori Tsohon Gwamnan Kaduna El-Rufai

July 28, 2025
Harin Sojojin Sama Ya Hallaka Manyan Shugabannin ISWAP A Borno

Harin Sojojin Sama Ya Hallaka Manyan Shugabannin ISWAP A Borno

July 28, 2025
Ministan YaÉ—a Labarai Ya Yi Jimamin Rasuwar Babban ÆŠan Jarida Leon Usigbe

Ministan YaÉ—a Labarai Ya Yi Jimamin Rasuwar Babban ÆŠan Jarida Leon Usigbe

July 28, 2025
Ƴansanda Sun Cafke Barayin Motoci 3 A Kano

Ƴansanda Sun Cafke Barayin Motoci 3 A Kano

July 28, 2025
Tinubu Ya Ƙaddamar Da Shirin Bai Wa Malaman Manyan Makarantun Nijeriya Rancen Miliyan 10

Tinubu Ya Ƙaddamar Da Shirin Bai Wa Malaman Manyan Makarantun Nijeriya Rancen Miliyan 10

July 28, 2025
An Kwashe Duk Dabbobin Tsohon Akanta-Janar

An Kwashe Duk Dabbobin Tsohon Akanta-Janar

July 28, 2025
Gwamnatin Kano Ta Kafa Kwamitin Bincike Kan Belin Dillalin Kwaya

Gwamnatin Kano Ta Kafa Kwamitin Bincike Kan Belin Dillalin Kwaya

July 28, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.