Shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin NPC Zhao Leji, ya ce zuba jari a kasar Sin tamkar zuba jari ne domin gaba, kasancewar babbar kasuwar kasar za ta ci gaba da haifar da babbar gajiya ga kowa.
Zhao, ya bayyana hakan ne cikin jawabinsa, yayin bude dandalin shekara shekara na Boao na nahiyar Asiya a yau Alhamis, a Boao na lardin Hainan dake kudancin kasar Sin.
- Kotu Ta Tsare Wani Mutum Kan Yi Wa ‘Yar Shekaru 11 Ciki A Legas
- Amurka Ba Ta Nuna Sahihanci Kan Batun Tsagaita Bude Wuta a Yankin Gaza
A jiya Laraba, Zhao Leji ya gana da ’yan kwamitin gudanarwa na dandalin Boao na nahiyar Asiya ko BFA, da wasu daga wakilan majalissar bayar da shawarwari ta taron, da kuma wasu muhimman abokan huldar taron na Boao.
Yayin ganawarsu, Zhao Leji ya ce taken dandalin na bana, wato “Asiya da duniya: kalubalen bai daya, da nauyaye-nauyaye kowa da kowa”, ya mayar da hankali ga shawo kan batutuwa dake jan hankulan sassan kasa da kasa, wanda hakan ke da muhimmanci a zahiri.
Ya ce a duniyar yau, kalubale daban daban, da rikice-rikice sun sarke da juna, to amma duk da haka, yayin da ake fuskantar kara tsanantar al’amura, haka kuma ya dace a kara azamar cimma daidaito, da goyon bayan juna da hadin gwiwa.
Zhao Leji ya kara da cewa, “Sin za ta samarwa duniya karin damammaki karkashin gajiyar sabbin sassan ci gabanta, kana za ta ci gaba da goyon bayan bunkasar dandalin na BFA. Daga nan sai ya yi fatan cewa, dandalin zai ba da babbar gudummawa ga wanzar da zaman lafiya, da ci gaban nahiyar Asiya da ma sauran sassan duniya baki daya. (Saminu Alhassan)