Mai magana da yawun ma’akatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana a yayin taron manema labarai na yau da kullum Larabar nan cewa, ziyarar da shugabar kasar Tanzaniya Hassan Samia Suluhu za ta kawo kasar Sin, ta nuna irin kyakkyawar abokantaka da amincewa da juna dake tsakanin Sin da Tanzaniya. Kasar Sin ta yi imanin cewa, ziyarar za ta kara ciyar da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa gaba.
Daga yau Laraba 2 zuwa 4 ga wata ne, shugabar Jamhuriyar Tanzaniya Samia Sulhu Hassan za ta kawo ziyarar aiki kasar Sin, ziyarar dake zama ta farko tun bayan da ta kama aiki. Kana ita ce shugabar Afirka ta farko da ta ziyarci kasar Sin, tun bayan kammala babban taron wakilan JKS karo na 20. (Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa)