Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya ce kwarya-kwaryar taron shugabannin APEC karo na 32, da ziyarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gudanar a kasar Koriya ta Kudu, sun bude babin yaukaka hadin gwiwar yankin Asiya da Fasifik, kuma hakan ya shaida nauyin dake wuyan Sin na babbar kasa a duniya.
Wang Yi, ya yi tsokacin ne a Lahadin nan, yayin taron manema labarai dangane da ziyarar da shugaban na Sin ya gudanar a Koriya ta Kudu. Ya ce cikin kwanaki uku, shugaba Xi ya halarci sama da taruka 10 na kasar Sin da wasu daidaikun kasashe, da na kasashe da dama, kuma wannan muhimmiyar tafiya mai nagarta, ta kara karfafa kyakkyawan yanayin makwaftaka da kawance, tare da cimma cikakkiyar nasara.
Daga nan sai ya bayyana yadda sassan kasa da kasa suka jinjinawa bulaguron na shugaba Xi, suna masu imanin cewa, Sin ta ingiza daidaito mai tasiri cikin yanayin duniya mai cike da rashin tabbas. (Saminu Alhassan)














