Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya kaddamar da fara aikin gina layin jirgin kasan da zai zagaye birnin Maiduguri da kewaye.
Wannan aiki shi ne irinsa na farko da wata daga cikin gwamnatocin jihohin Arewacin Nijeriya 19 ta kaddamar.
- Babbar Kasa Mai Farar Aniya: Shin Har Yanzu Akwai Masu Son Lalata Dangantakar Sin Da Afrika?
- Xi Ya Ce Sin Ta Dukafa Wajen Ganin Duniya Na Amfana Da Magungunan Gargajiya Yadda Ya Kamata
Kashin farko na aikin zai fara ne da gina tashoshin jirgin kasa 12 a birnin Maiduguri, da zai karade manyan kasuwanni da makarantu da wuraren taron jama’a da na harkokin tattalin arziki.
Aikin, za a iya fadada shi ya kai yankunan kananan hukumomi a nan gaba.
Kazalika, aikin zai taimaka wajen saukaka jigilar fasinjoji da kayayyaki, tare da buda hada-hadar tattalin arziki da yankunan da ke loko a jihar.
Da yake rangadin duba tashoshi da hanyoyin farko da aka tsara na aikin jirgin kasan tare da kamfanin gine-ginen EEC da zai taimaka wajen gudanar da aikin, Kwamishinan ayyuka na jihar, Aliyu Muhammad Bamanga, ya ce ana aikin nazarin wuraren da aikin zai bi da auna illolin da aikin zai iya yi wa muhalli.
Sannan ya ce suna tuntubar al’ummomin da aikin zai bi ta yankunansu domin tabbatar da nasarar aiwatar da shi.