Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya amince da daukar likitoci 40 ‘yan asalin jihar da suka yi karatun zama likita don fara aiki a yankunan karkara na Jiihar ba tare bata lokaci ba.
Zulum, ya bayyana haka ne a yayin da ya karbi bakoncin sabbin likitocin da suka kammala karatunsu a jami’o’i daban-daban na kasar nan.
- Hajjin 2022: Matawalle ya bukaci maniyyata su yi wa Najeriya addu’a ta musamman kan matsalar tsaro
- ‘Yan Sanda Sun Ceto Matar Shugaban APC Na Jihar Neja Da Aka Sace A Borno
Ya ce, an amince da a dauki likitocin ne a matsayin matakin kara inganta harkar lafiya a fadin jihar.
A jawabinsa, babban sakataren ma’aikatar lafiya na Jihar Borno, Dakta Muhammad Nguluze, ya tabbatar wa da gwamnati cewa, a shirye likitocin suke su yi wa jihar su ta asali aiki a ko ina a fadin jihar don tallafa wa al’ummarsu.
Nguluze ya kuma kara da cewa, wasu daga cikin likitocin na daga cikin wadanda gwamnatin jihar ta dauki nauyin karatunsu a Sudan da Masar.