Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya gabatar da kasafin kudin 2023 na Naira biliyan 234 ga majalisar dokokin jihar domin amincewa.
Gwamna Zulum ya ce, wannan kasafin kudin 2023 zai gudana ne wajen kammala dukkan ayyukan da jihar ta fara a shekarar 2022, musamman kuma da aiwatar da sauran aikace-aikacen da Ma’aikatu, Cibiyoyi da Hukumomi a kasafin kudin.
- Miji Ya Hallaka Matarsa A Kan Ruwan Sha A Legas
- Kwastam Ta Kama Mutane 4 Kan Zargin Fasa-Kwauri, Sun Tara Sama Da N179m A Katsina
Bugu da kari kuma ya kara da cewa, kasafin kudin bana ya ragu idan an kwatamta da kasafin 2023 da kimanin kashi 12.31 cikin dari na Naira biliyan 270 na shekarar 2022.
Gwamnan ya sake bayyana cewa an ware Naira biliyan 144.2 a matsayin manyan ayyukan da kasafin zai aiwatar a wannan shekara, yayin da ayyukan gwamnati na yau da kullum aka ware musu Naira biliyan 90.66.
Ya ce: “Za a aiwatar da kasafin ne daga kudaden shigar da jihar ke samu na yau da kullum na Naira biliyan 137.85, kana da kason Naira biliyan 67.98 daga gwamnatin tarayya.”
A hannu guda kuma, kasafin zai samu kudinsa ta hanyoyin kudin shiga na cikin gida na Naira biliyan 33.2 da kuma kudaden haraji na musamman na kimanin Naira biliyan 30.2.”
A nashi bangaren, kakakin Majalisar Dokokin Jihar Borno, Hon. Abdulkarim Lawan, ya tabbatar wa gwamnan cewa majalisar mai wakilai 28 za ta gaggauta amincewa da kasafin kudin, don bai wa bangaren zartaswa damar gudanarwa da al’ummar jihar muhimman ayyukan ci gaba.