Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ba da umarnin a gaggauce a kama Bukar Modu, malamin tsangayar da aka hango shi a faifan bidiyo yana dukan wani karamin yaro, Bashir Gaji, wanda ya haifar da muhawara mai zafi.
Jami’an tsaro sun kama Bukar Modu a daren Asabar a unguwar Umarari da ke Maiduguri. Gwamna Zulum ya bayar da umarnin a kawo shi fadar gwamnati domin gurfanar da shi bisa zargin cin zarafi.
- ‘Yan Boko Haram Na Ci Gaba Da Mamaye Sassan Jihar Borno -Zulum
- Bam Ya Halaka Mutum 8, Ya Jikkata Wasu Da Dama A Borno
Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci duk wani nau’i na cin zarafi ko zaluntar yara ba. Ya bai wa hukumomi umarnin ɗaukar matakin gaggawa don gurfanar da wanda ya aikata wannan laifi a kotu.
Gwamna Zulum ya kuma bayar da umurnin Ma’aikatar harkokin mata da ci gaban al’umma ta tsara shirye-shiryen wayar da kan al’umma don ilimantar da iyalai da malamai kan haƙƙin yara.
A wannan yanayi, Gwamna Zulum ya gana da Bashir Gaji, yaron da aka ci zarafi, a Fadar Gwamnatin Jihar dake Maiduguri. A lokacin ganawar, Gwamnan ya bai wa yaron kyautar gida da tallafin karatu domin taimaka masa wajen ci gaba da karatunsa, sakamakon iyayen Bashir Gaji suna zaune ne a sansanin yan gudun hijira a Monguno bayan rasa mahaifinsa a rikicin Boko Haram.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp