Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum ya raba kudi naira miliyan 255,650,000 da buhunan shinkafa 5,513 mai nauyin kilo 50 ga jami’an rundunar hadin gwiwa ta farar hula (Civilian Task Force) da mafarauta da ke yaki da mayakan Boko Haram tare da jami’an tsaro a jihar.
Gwamna Zulum ya bayyana kyautar ne a dakin taro na Multipurpose Hall na gidan gwamnati da ke Maiduguri a ranar Laraba.
- Da Dumi-Dumi: Majalisa Ta Amince Da Kudirin Bai Wa Dalibai Bashi
- Yunkurin Yin Katsa Landan Ba Zai Dakile Ci Gaban Yankin HK Ba
Kimanin jami’an CJTF 5,523 da mafarauta da ke aiki a cikin Maiduguri da Jere, ciki har da wadanda ke karbar albashin gwamnati da kuma masu aikin sa kai ne suka ci gajiyar shiri.
Kowanne daga cikin 4,513 da ke karbar albashin wata-wata daga gwamnati an ba shi buhun shinkafa 50kg da tsabar kudi N50,000 yayin da masu aikin sa kai 1,000 kowanne ya samu buhun shinkafa 50kg da tsabar kudi N30,000.
Gwamna Zulum ya nuna jin dadinsa ga masu aikin sa kai bisa sadaukarwar da suka yi wajen ganin an samu zaman lafiya a jihar.