Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya yi ta’aziyya ga dakarun haɗin gwuiwa (MNJTF) kan harin da Boko Haram ta kai a Wulgo, wata ƙaramar hukuma a kan iyaka da Jamhuriyar Kamaru. Zulum ya kai ziyarar ta’aziyya ga dakarun Kamaru a ƙarƙashin Sashen 1 na MNJTF a ranar Alhamis.
A lokacin ziyarar, Gwamnan Zulum ya miƙa ta’aziyyarsa ga gwamnatin Jamhuriyar Kamaru da al’ummarta kan wannan abin alhini. Zulum ya bayyana cewa yana cikin garin Wulgo, wanda yake kimanin kilomita 15 daga Gamboru Ngala, inda ya samu tarɓa daga kwamandan MNJTF, Janar Godwin Michael Mutkut.
- Zulum Ya Gana Da Yaron Da Aka Ci Zarafi, Ya Ba Shi Gida, Tallafin Karatu
- Gwamna Zulum Ya Ƙaddamar Da Aikin Gina Titi Da Gadar Sama Ta Huɗu A Borno
Gwamna Zulum ya jaddada cikakken goyon bayan Gwamnatin Tarayya ta Nijeriya ga MNJTF da hukumomin Kamaru wajen yaƙi da ta’addanci a yankin tafkin Chadi. Ya kuma yi alƙawarin cewa Nijeriya za ta ci gaba da ba da dukkan tallafin da ake buƙata domin kawo zaman lafiya a yankin.
A cikin ziyarar, Gwamnan Zulum ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar Borno za ta ci gaba da tallafawa dakarun da ke yaki a filin daga. Zulum ya samu rakiyar sanatan Borno ta tsakiya, Sanata Kaka Shehu Lawan, da wasu daga cikin masu ba shi shawara.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp