Ministan Tsaro, Bello Muhammad Matawalle, ya ce zuwan tsoffin ’yan wasan ƙwallon ƙafar ƙungiyar Barcelona zuwa Nijeriya alama ce ta cewa ƙasar na samun ci gaba wajen dawo da tsaro da kwanciyar hankali.
Matawalle ya faɗi haka ne a Abuja ranar Juma’a, a wata sanarwa da mataimakinsa na yaɗa labarai, Ahmad Dan-Wudil, ya fitar.
- Gwarzon Kamfanin Fasahar Kuɗaɗe Na Shekarar 2025, Opay Nigeria
- Mata Ne Ginshikin Ci-Gaban Al’umma – Gimbiyar Dange
A cewarsa, wannan ziyara ta nuna cewa duniya na ganin irin ƙoƙarin da Gwamnatin Tarayya ke yi wajen tabbatar da tsaro a ƙasar.
“Zuwan tsoffin ’yan wasan Barcelona zuwa Nijeriya alama ce ta cewa ana samun gagarumin ci gaba wajen dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali,” in ji Matawalle.
Ya ƙara da cewa hakan ya tabbatar da cewa Nijeriya ta koma jerin ƙasashen da ake iya gudanar da manyan taruka da wasanni lafiya.
“Muna godiya ga sadaukarwar da sojoji da hukumomin tsaro ke yi. Wannan wasa tsakanin tsoffin ’yan wasan Barcelona da tsoffin ’yan wasan Afirka shaida ce ta nasarorin da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta samu wajen dawo da zaman lafiya,” in ji shi.
Tsoffin ’yan wasan Barcelona sun isa Nijeriya domin buga wasa da tsoffin ’yan wasan Afirka a filin wasa na Moshood Abiola da ke Abuja, a ranar Asabar, 25 ga watan Oktoba, 2025.
Yayin da Matawalle ke tarbarsu a ofishinsa, ya miƙa saƙon maraba da fatan alheri ga tawagar a madadin Gwamnatin Tarayya da al’ummar Nijeriya, inda ya yi musu fatanalheri.












