Ƙasashen da ke gefen Sahara sun yi asarar dala biliyan 1.56 sakamakon katsewar Intanet a shekarar 2024, a cewar wani sabon rahoto na ‘Top10vpn’, wani shafin yanar gizo da ke leke a tsakanin kasa da kasa.
Hakan shi ne kashi 19 cikin 100 na jimillar dala biliyan 7.69 da aka yi asara sakamakon katsewar Intanet a duk duniya, wanda kuma hakan ya nuna cewa, an samu ragowa da kashi 10 cikin 100 daga dala biliyan 1.74 da aka samu a shekarar 2023.
- Rahoto Ya Nuna Yadda Kanana Da Matsakaitan Kamfanonin Sin Ke Tafiya Cikin Tagomashi
- Binciken Jami’ar Bayero Ya Gano A Hoton Yatsa Za A Iya Gane Mai Cutar Daji – Farfesa Darma
A cewar rahoton, an samu katsewar Intanet sau 28 a kasashe 28. Daga cikin Ƙasashen da lamarin ya shafa, 13 ƙasashen Afirka ne – Sudan, Habasha, Kenya, Aljeria, Guinea, Mauritania, Senegal, Mozambique, Chadi, Mauritius, Tanzania, Papua New Guinea, da Equatorial Guinea.
Rahoton ya keɓe Nijeriya daga cikin Ƙasashen da lamarin ya afku a shekarar 2024 duk da cewa, kasar tana daga cikin Ƙasashen da ke gefen Sahara