Hadaddiyar kungiyar kanana da matsakaitan kamfanonin Sin ta sanar a yau cewa, a rubu’i na 4 na shekarar 2024, ma’aunin ci gaban harkokin kanana da matsakaitan kamfanonin kasar Sin ya kai maki 89, jimillar da ta karu da maki 0.1 bisa ta rubu’i na 3 na bara.
Rahoton da aka gabatar ya nuna cewa, an samu ci gaba a dukkan fannonin yawan kayayyakin da ake neman saya, da aikin samar da kayayyaki, da bangaren sayarwa, da na ajiyar kaya, na kanana da matsakaitan kamfanoni na kasar Sin. Kana an fi samu ci gaba a bangaren masana’antun hada kayayyaki, da sana’ar samar da hidimomi ga al’umma.
- Karo Na 35 Ne Ministan Harkokin Wajen Sin Ya Kammala Ziyararsa Ta Farko A Kowace Shekara A Afirka Cikin Nasara
- Sin Da Afirka Za Su Ci Gaba Da Aiwatar Da Tsare-tsaren Ayyukan Hadin Gwiwa 10
Ban da haka, an ce an samu saukin matsin lambar da kamfanonin Sin suke fuskanta kan kudaden da suke kashewa, musamman ma a sana’o’i 5 da suka hada da masana’antu, da aikin gini, da aikin sayar da gidaje, da bangaren sayar da kayayyaki, gami da na tsara manhajoji da sadarwa.
Hakazalika, rahoton ya nuna an samu karuwar injuna da na’urorin da kamfanonin suke amfani da su wajen samar da kayayyaki, inda yawan kamfanonin da suke aiki da dukkan injunansu wajen hada kaya ya kai kaso 39.4%, adadin da ya karu da kaso 6.7% idan aka kwatanta da na rubu’i na 3 na bara. (Bello Wang)