Kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta ce jam’iyyar ADC da kawancen ‘yan adawa a Nijeriya ba su da ƙarfin da za su iya kayar da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.
Ƙungiyar ta zargi wasu ‘yan takarar shugaban ƙasa na ADC a matsayin masu matsala da hannu dumu-dumu cikin cin hanci da rashawa da ƙoƙarin karɓe iko daga gwamnati ta kowane hali.
- Ohanaeze Ndi Igbo Ta Yi Allah-Wadai Da Dakatar Da Emefiele
- An Kaddamar Da Alkur’ani Da Aka Fassara Zuwa Harshen Igbo A Abuja
Ohanaeze ta bayyana cewa, jam’iyyar ADC cike take da ‘yan siyasa masu rauni da son mulki ta karfi da yaji, kuma ba za su iya kayar da Tinubu ba.
Kungiyar ta kuma soki Atiku Abubakar kan abin da ya aikata wa yankin Kudu Maso Gabas a zaɓen fidda gwani na PDP a 2022, da kuma Nasir El-Rufai kan abin da ya faru a Kudancin Kaduna. Haka zalika, sun buƙaci Rotimi Amaechi da ya bayyana dalilin da yasa ya fifita sauran yankuna wajen aikin layin dogo fiye da yankin Gabas.
Ohanaeze ta jaddada buƙatar cewa ba za ta mara wa ADC baya ba a zaɓen 2027 ba, kuma Igbo sun amince da ci gaba da goyon bayan Shugaba Tinubu. Ƙungiyar ta ce ministoci da gwamnoni daga yankuna daban-daban sun samu amincewar jama’a, kuma Tinubu zai samu nasara a 2027. Ta kuma buƙaci a binciki zargin cin hanci a hukumar NDDC game da tuhumar da ake yi wa matar Amaechi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp