A safiyar jiya Alhamis ne ‘yan bindiga suka tare babbar hanyar Gusau–Funtua a Jihar Zamfara tare da yin garkuwa da matafiya kimanin 150.
‘Yan bindigar, da suka iso a kimanin babura 50 tare da mutane uku a kowanne, sun kafa shingen tare hanya a yankin Tazame, inda suka kama fasinjoji da dama. Shaidu sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun fara aikin su tun kusan karfe 7 na safe har zuwa karfe 9 na safe, yayin da dakarun soji suka yi ƙoƙarin kai farmaki amma ba su samu nasarar karɓe iko da hanyar ba.
- An Tura Karin Dakaru A Zamfara Yayin Da Wa’adin Harajin Turji Na Miliyan 30 Ya Cika
- Gwamnan Zamfara Ya Kaddamar Da Rabon Naira Biliyan 11 Na Bunkasa Ilimin Mata A Jihar
Yusuf Tsafe, wani fasinja da suka tsaya a hanyar, ya bayyana halin da aka shiga, inda ya ce har lokacin ‘yan bindigar na nan suna shiga da mutane cikin daji. A yanzu haka, Sojoji na ƙoƙari don tabbatar da tsaron yankin, sai dai shima titin Magazu–Kucheri, wanda ya haɗa Gusau da Funtua, ya kasance a kulle sakamakon shingen ‘yan bindigar.
Jihar Zamfara, kamar sauran sassan arewa maso yammacin Nijeriya, na ci gaba da fama da yawaitar satar mutane da hare-haren ‘yan bindiga. Wannan lamarin ya biyo bayan cikar wa’adin neman kudin fansa da wani shahararren shugaban ‘yan bindiga, Bello Turji, ya nema a ƙaramar hukumar Zurmi, wanda hakan ya kara haifar da tsoro a yankin.
Hukumomi sun tura ƙarin dakarun Soji don magance matsalar.