Rundunar Ƴansandan jihar Adamawa ta bayyana cewa jami’anta sun gano motoci biyu da aka sace, tare da kama wani mutum mai suna Musa Suleh da ake zargi da satar.
Mai magana da yawun rundunar a jihar, SP Suleiman Yahaya, ya ce nasarar ta samu ne sakamakon bayanan sirri da DPO na Yola Division ya samu, wanda ya kai ga cafke wanda ake zargin a Jambutu Motor Park da ke ƙaramar hukumar Yola ta Arewa.
- Jami’in Tsaro Ya Mayar da Dala 505 Da Riyal 30 Da Ya Tsinta A Yola
- Sin Ta Sanar Da Cimma Nasarar Dashen Huhun Alade A Jikin Bil’Adama
A cewarsa, wanda ake zargin ya amsa cewa ya saci wata mota ƙirar Toyota Starlet mai lambar YLA-420 mallakar wani Babawo Abubakar na Ngurore, Yola ta Kudu. Haka kuma an gano wata mota ƙirar Toyota Starlet mai launin kore mai lambar JAL-861 CL a hannunsa, wadda bai gabatar da takardu ko hujjar mallaka ba.
Kwamishinan Ƴansanda na jihar, CP Dankombo Morris, ya bayar da umarnin a miƙa shari’ar ga sashen binciken manyan laifuka na rundunar domin zurfafa bincike da gano asalin motocin. Rundunar ta kuma buƙaci jama’a da su riƙa ba da bayanai cikin lokaci kan duk wani motsi da ya saɓa al’ada a unguwanninsu, tare da tabbatar da ƙudirin ta na ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Rundunar ta ce bayan kammala bincike, ana sa ran gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu domin fuskantar shari’a.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp