Wani matashi a Jihar Zamfara wanda ƙani ne ga ɗan Majalisar jiha ya shaƙi iskar ƴanci bayan kwashe lokaci mai tsawo a hannun ƴan bindiga.
Rahotanni daga masani kan harkokin tsaro a tafkin Chadi, Zagazola Makama, ya ce, an yi garkuwa da shi ne a lokacin da yake kan hanyarsa ta komawa makaranta, inda a nan ne ya yi arangama da dandazon ƴan bingida ɗauke da muggan makamai.
- Ramadan: Sanata Abdulaziz Yari Zai Raba Tirela 358 Na Kayan Abinci A Jihar Zamfara
- Ministan Ayyuka Ya Jinjina Wa Gwamnan Zamfara Kan Ayyukan Sabunta Birane
Shi dai matashin ƙani ne ga ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Maru ta Arewa a Majalisar Jiha.
Idan za a tunawa a watannin ƙarshe na shekarar 2023, ƴan bindiga sun yi awon gaba da dalibai mata da ke karatu a Jami’ar Gusau babban birnin Jihar Zamfara.
Dama dai Jihar Zamfara na ɗaya daga Jihohin Arewa da ke fama da matsanancin matsalar tsaro da ta jima tana addabar yankin, ta kuma yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama da kuma raba wasu dubbai da muhallansu.