ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ƙarin Harajin Amurka Zai Illata Tattalin Arziƙin Duniya

by Rabi'u Ali Indabawa
9 months ago
Haraji

A halin da ake ciki yanzu haka, yanayin tattalin arzikin duniya na fuskantar guguwar rashin tabbas, a gabar da Amurka ke kara tsaurara matakan kakaba haraji kan hajojin da ake shigarwa kasar daga wasu kasashen duniya, matakan da masana tattalin arziki daga sassan kasa da kasa ke ta suka, tare da bayyana su a matsayin illa da ka iya dakile ci gaban tattalin arzikin duniya baki daya, baya ga ingiza hauhawar farashi, da gurgunta tsarin cinikayyar kasa da kasa da hakan zai haifar.

Bisa halin da ake ciki, masu masana tattalin arziki na ganin matakan nan na kakaba karin haraji da Amurka ke aiwatarwa, za su ci gaba da zama barazana ga daidaiton tattalin arzikin duniya, kuma ko da kaso kadan daga cikin su Amurka ta aiwatar, hakan na iya tauye hasashen da aka yi na ci gaban tattalin arzikin duniya, tare da haifar da hauhawar farashi a Amurka ita kanta.

  • Kasar Sin Za Ta Kara Sanya Harajin Fito Na Kaso 34% Kan Dukkan Kayayyakin Da Take Shigowa Daga Amurka
  • Yadda Wata Gada Ta Balle Ta Kashe Mutum 60 A India

Idan mun duba irin wadannan matakai da Amurka ta dauka a baya, da wadanda take dauka a yanzu, ma iya cewa a wannan karo gwamnatin Amurka mai ci ta rungumi manufofi da tsare-tsare mafiya haifar da rashin tabbas sama da na kowane lokaci a baya, ta yadda lamarin ya zamo babban kalubale ga yanayin kasuwancin duniya.

ADVERTISEMENT

Wani abun lura ma shi ne yadda gwamnatin Amurka take ta kokarin dorawa kasar Sin laifinta na gazawa, da koma-bayan da take fuskanta ta fannin bunkasar tattalin arziki, zarge-zargen da ko shakka ba su da wata makama.

A daya hannun kuma, duk da cewa karin harajin na gwamnatin Amurka mai ci na iya rage givin cinikayya tsakaninta da Sin, amma kuma hakan zai haifar da karuwar givin cinikayya tsakanin Amurka da wasu karin kasashen duniya, wanda hakan zai sabbaba koma-baya ga tattalin arzikin duniya baki daya.

LABARAI MASU NASABA

Yadda Aka Gudanar Da Taron Tuna Shekara 20 Da Rasuwar Dr Bala Usman

Gamayyar kungiyoyin Seyi Tinubu (STSG) Na Shirin Gangamin Taronta Na Kasa

Masu fashin baki da dama na da ra’ayin cewa, tabbas illar wannan mataki na Amurka zai koma kanta, inda wasu daga sassan raya tattalin arzikin kasar kamar na albarkatun gona, da makamashi za su iya fuskantar matsin lamba mai tsanani.

Yayin da wasu sassan kamfanonin kasar kuma ka iya fuskantar raguwar ribar da suke samu da kaso mai yawa, sakamakon karin kudaden hajojin da ake samarwa a masana’antun kasashen da Amurkan ta karawa haraji.

La’akari da wadannan illoli, kamata ya yi Amurka ta yi karatun ta nutsu, ta dakatar da matakan kakaba haraji marasa ma’ana, kana ta koma teburin tattaunawa, domin warware duk wani savani na kasuwanci da cinikayya tare da dukkanin sassan da batun ya shafa, ta yadda za a gudu tare a tsira tare.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yadda Aka Gudanar Da Taron Tuna Shekara 20 Da Rasuwar Dr Bala Usman
Kananan Labarai

Yadda Aka Gudanar Da Taron Tuna Shekara 20 Da Rasuwar Dr Bala Usman

September 26, 2025
Gamayyar kungiyoyin Seyi Tinubu (STSG) Na Shirin Gangamin Taronta Na Kasa
Kananan Labarai

Gamayyar kungiyoyin Seyi Tinubu (STSG) Na Shirin Gangamin Taronta Na Kasa

May 23, 2025
Gwamnati Ta Ware Wata 14 Don Kammala Aikin Hanyar Abuja Zuwa Zariya
Kananan Labarai

Gwamnati Ta Ware Wata 14 Don Kammala Aikin Hanyar Abuja Zuwa Zariya

April 18, 2025
Next Post
Bruno Fernandes Ba Na Sayarwa Ba Ne – Ruben Amorim

Bruno Fernandes Ba Na Sayarwa Ba Ne - Ruben Amorim

LABARAI MASU NASABA

Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

December 21, 2025
Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.