Al’amarin yadda ‘yan ta’adda suke cin karensu babu ko babbaka abin yana da matukar daure kai domin kuwa suna yin abubuwan da suka ga dama, su kashe manoma, su kona gonakinsu, ko su kwashe masu kayan amfanin gonarsu, kai sai dai abinda suka ga damar yi. Yanzu dai ba karamar illa ko matsala suke bada gudunmawa ba ta wajen karancin abinci.
Gaba dayan Jihohin Arewa kadan ba su fusknatar irin wannan halin in ma da akwi su, sai dai kawai ace irin cin fuskar da suke yi a wadancan wuraren sun sha bamban dana wadansu wurare sai daia yi fatan Allah ya taiamaka mana wajen kawo karshen ta’asar da suke yi, da a karshe take samar da karancin abinci.
- Yanayin Cin Abinci Da Baccin Annabi Muhammadu (SAW)
- Gwamnatin Bauchi Ta Kaddamar Da Kwamitin Adana Kayan Abinci
Ta irin hakan ne yanzu an samu dalilai da suka sa aka kona gonakin masara na wasu al’umma a karamar hukumar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna, barnar da ‘yan ta’adda ne suka yi ta.
Shugaban kungiyar ci gaban masarautar Birnin-Gwari (BEPU), Ishak Usman Kasai, wanda kuma har ila yau shine shugaban kungiyar al’ummomin da suke bakin iyaka, a hirar da yayi da manema labarai ya bayyana cewa da akwai wani abinda ya faru wanda ya shafi yarjejeniyar da aka yi ta zaman lafiya.
Kamar yadda yace, “Wurin da jamia’an tsaro suka kawo zaman lafiya a kokarin da suke yi shine babbar hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari.Amma idan ana maganar kauyuka ne babu wani abinda aka yi a wuraren da za ‘a iya cewa sun taimaka hare- haren sun ja da baya.
“Dan haka abinda ya far ranar Lahadi ta makon daya gabata inda wasu ‘yan ta’adda suka kona wasu gonaki kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari, shine wasu wurare kusa da Kwoga, Zoko da kuma Gayam. Wurin da akwai wani azabibin shugaban’ dan ta’adda wanda ake kira da suna Yellow Janbros.
“Akwai wani jami’in soja a wurin wanda yana yin duk abubuwan da suka kamata domin ya samu hanyar gamawa da ‘yan ta’addar wadanda suke bi ta hanyar shanu zuwa Zamfara, ta Birnin Gwari zuwa Jihar Neja domin kawai su je su kai hare- hare.
Jami’in soja shi da tawagar ta sa sun samu gamawa da wasu ‘yan kungiyar Yellow Janbros. Mako biyu da suka wuce, jami’in sojan ya jagoranci tawagarsa inada suka kai samame lokacin da ‘yan ta’addar suke wucewa daga Neja domin su shiga Birnin Gwari.
“Sanadiyar abinda sojojin suka yi masu ne yasa suka saw a gonakin masarar wuta ranar Lahadi kusa da wurin. Sun yi hakan ne inda suka fadawa mutanen da suke wurin, su zo su sake yin wata yarjejeniyar zaman lafiya, ko kuma su ci gaba da kai masu hare- hare.Da suka ji hakan ne fa sai su al’ummar wurin suka fara tunanin hanyoyin da za su taimakawa jami’an soja su gama da ‘yan ta’adda.
“Maganar gaskiya abinda ya kawo tsaikon rashiun zaman lafiya ya fara ne tun arangamar da suka yi da soja suka yi masu luguden wuta, da lalacewar yarjejeniyar zaman lafiya ta sa su ‘yan ta’addar suka zafafa kai hare- hare a gonakin manoma”.
Kafin dai akai harin na ranar Lahadi, “akwai wani Malamin addini daga sashen Bauchi da Gombe, da ake kiransa Azadu Sunnah, wanda ya zo Birnin Gwari ranar Asabar saboda a samu ayi lamarin daya shafi yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin ‘yan ta’adda da mutanen garin, amma kuma ranar Lahadi sai su ka kai wa mutanen wuriin hari.
“Idan ko muddin dai ana bukatar garin Birnin Gwari da gaba dayan sashen Arewa maso yamma su samu zaman lafiya, kamata yayi gwamnati ta tura sojoji zuwa dajin Kuduru, tsakanin Chikun da Birnin Gwari, a tura soja zuwa dajin Kamuku da dajin Kuyanbana tsakanin Dan Sadau a Jihar Zamfara da Kaduna , aje dajin Kuzamani akan iyaka Kaduna da Neja”.
Sai dai kuma a dukkan wuraren nkamar yadda ya jaddada, “A dukkan wuraren akwai kungiya- kungiya ta ‘yan ta’adda wadanda suka kai muatane zuwa dazuzzukan, ga shi kuma babu isassun jami’an tsaro a wuraren da suke da hatsari. Don haka akwai bukatar a shirya rundunar tsaro ta hadin gwiwa tskanin Jiha da Jiha a Jihohin, Kaduna, Neja da Zamfara.Abinda ya kamata ayi ke nan ba kawai a tsaya kan hanya ba ko kuma wasu wuraren al’umma .