Karamin Ministan Albarkatun Ruwa da Tsaftar muhalli, Alhaji Bello Goronyo, ya ce, kudurin Shugaba Bola Tinubu kan batun samar da abinci ba wai kawai alkawari ba ne a fatar baki kadai ba, ya ba abun muhimmanci.
Da yake jawabi a jihar Sokoto a ranar Lahadi a yayin ziyarar duba aikin da ake yi na madatsar ruwa a Dam din Goronyo, Ministan ya jaddada mahimmancin ‘yan kwangilar na sauke nauyin da ke kansu.
- Tinubu Zai Kaddamar Da Shirin Bayar Da Lamunin Dalibai A Ranar Alhamis
- Ku Yi Haƙuri Da Gwamnatin Tinubu – Shettima
Goronyo ya bayyana cewa mambobin majalisar zartaswa ta kasa suna kokari wajen sa ido kan ayyukan ma’aikatu da hukumomi don tabbatar da ingancin aiki sosai.
“Lokacin sakaci da aiki ya wuce, mun himmatu kwarai wajen sanya ido a kan ‘yan kwangila da yadda suke gudanar da ayyukansu. Ba za mu baka aiki ka je gida kana hutawa ba bayan mun biya ka kudin aikinka.
“Ba mu da sauran sukuni har sai ‘Yan Nijeriya sun ci gajiyar mulkin dimokwaradiyya a karkashin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu,” Cewar minista.