Ƙungiyoyin farar hula (CSOs) a Kano sun buƙaci a gaggauta dakatarwa da gurfanar da jami’an gwamnati da aka zarga da hannu a badaƙalar rashawa da ta kai biliyoyin Naira. Wannan kiran ya biyo bayan rahotannin da suka nuna cewa Daraktan sashin huldar fadar Gwamnati, Abdullahi Ibrahim Rogo, ya karkatar da Naira biliyan 6.5 tsakanin Nuwamba 2023 da Fabrairu 2025 ta hannun kamfanoni daban-daban ta hanyar kwangilolin bogi.
Haka kuma, hukumar ICPC ta kammala bincike a wata badaƙalar Naira biliyan 1.02 da ya shafi Shugaban hukumar Zaɓe ta jihar Kano (KANSIEC), Farfesa Sani Lawan Malumfashi, Sakataren hukumar Anas Mustapha, da Darakta Ado Garba, inda suka fitar da kuɗi daga asusun hukumar zuwa kamfani mai zaman kansa duk da cewa an biya ma’aikatan wucin gadi ta hanyar bankuna.
- Tanko Yakasai Ya Nuna Takaici Kan Rashin Samar Da Kamfanin Sarrafa Fata A Kano Kamar Na Legas
- Akwai Katin Zaɓe Fiye Da Dubu 367 Da Ba A Karɓa Ba A Kano – INEC
A cikin wata sanarwa da ƙungiyoyi 20 suka sanya hannu, sun bayyana wannan zargi a matsayin babbar alama ta cin hanci da rashawa da ke barazana ga tafiya da mulki, da tattalin arziƙi, da kuma amincewar jama’a da gwamnati. Sun ce irin wannan ɓarna tana rage zuwan masu zuba jari da karya ƙwarin gwuiwar matasa kan amana da cancanta.
Ƙungiyoyin sun buƙaci a gurfanar da duk wadanda aka zarga, a gudanar da bincike na musamman kan dukkan ma’aikatu da hukumomin jiha, a ƙarfafa rawar majalisar dokoki wajen sa ido, da kuma samar da kariya ga masu fallasa gaskiya. Haka zalika, sun buƙaci kafa dandalin tattaunawa da NGOs da shugabannin al’umma don ƙarfafa mulkin da zai mayar da hankali ga jama’a.
A cewarsu: “Jihar Kano na tsaye a kan tsauni. Ko dai mu fuskanci cin hanci kai tsaye mu dawo da amana a shugabanci, ko kuma mu bari mu faɗo cibiyoyinmu da makomar ‘ya’yanmu ta tuguje,” in ji sanarwar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp