Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya zargi jam’iyyun adawa da haɗa kai da wasu ƙasashen waje wajen yaɗa labaran ƙarya cewa ana kisan Kiristoci a Nijeriya, yana mai cewa hakan “adawa ce da ta wuce gona da iri.” Wike ya bayyana haka ne a hirar da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels TV, inda ya mayar da martani kan kalaman Shugaban Amurka, Donald Trump, wanda ya zargi gwamnati da aikata kisan kiyashi kan Kiristoci.
Wike ya ce kalaman Trump sun dogara ne da siyasa da ƙarya, yana mai cewa gwamnati ba ta nuna bambancin addini. “Shugaban tsaro Kirista ne, IGP Kirista ne, SGF ma Kirista ne. To ta yaya gwamnati irin wannan za ta zartar da manufofin kisan Kiristoci?” in ji shi. Ya ƙara da cewa, matsalar tsaro da ake fuskanta ta shafi Kiristoci da Musulmai baki ɗaya, ba wani addini guda ba.
- 2027: Wike Ya Gargaɗi PDP Kan Zawarcin Peter Obi
 - PDP Ta Dage Kan Gudanar Da Taronta Duk Da Sabbin Sharuɗɗan Da Ɓangaren Wike Ya Gindaya
 
Tsohon gwamnan jihar Ribas ya kuma kare Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa shugaban ƙasa ba mai tsattsauran ra’ayi ba ne. “Tinubu ya auri Kirista, kuma ya nuna ƙarfin hali wajen tabbatar da zaman lafiya tsakanin addinai. To me yasa za a ce yana da hannu wajen kisan Kiristoci? Wannan siyasa ce da ta wuce gona da iri,” in ji Wike.
Ya kuma tuna yadda irin wannan dabarar aka yi amfani da ita a 2015 domin ɓata tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, inda ƴan adawa suka yi amfani da labaran ƙarya wajen jawo rikicin addini. Wike ya yi gargaɗin cewa adawa na ƙoƙarin maimaita irin wannan dabarar ne yayin da ake tunkarar zaɓen 2027.
A cewar Wike, zargin da ake yi wa gwamnati a yanzu ba su da tushe, domin irin waɗannan kashe-kashe sun faru tun kafin Tinubu ya hau mulki. “A lokacin da aka sace ’yan matan Chibok ko lokacin kashe-kashen Benue, Tinubu ba shi ne shugaban ƙasa ba,” in ji shi. “Ba sai na zama Kirista ko Musulmi ba kafin in damu da mutuwar mutane, amma a yau, tabbas adawar ƴan siyasa ta wuce gona da iri.”
			




							








