An samu sabon zaman tattaunawa tsakanin jami’an tsaro da tubabbun ƴan bindiga a fadin Jihar Katsina, inda aka samu tabbacin dakatar da hare-hare a ƙananan hukumomi guda biyar na jihar.
Tattaunawar zaman lafiyar, wadda ta gudana a ƙauyen Kakumi da ke ƙaramar hukumar Bakori, ta haɗa da: ƴan bindiga da wakilan ƙananan hukumomi guda biyar da abin ya shafa — Bakori, da Kankara, da Funtua, da Kafur, da Malumfashi.
- Gwamnatin Katsina Ta Rufe Makarantu 32 Masu Zaman Kansu Da Ba Su Da Lasisi
- Dan Takarar Gwamnan Katsina A NNPP Ya Ba Da Tallafin Miliyan 50 Ga ‘Yan Gudun Hijira
Manufar tattaunawar ita ce ƙarfafa ƙoƙarin samar da zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin al’ummomi da ƴan bindigar da suka amince su ajiye makamai. Rahotanni daga yankin sun nuna cewa shugabannin ƴan bindigar sun yi alkawarin dakatar da kai dukkan hare-hare a cikin waɗannan yankuna daga ranar Lahadi, 12 ga Oktoba.
Wannan mataki na zaman lafiya yana cikin shirin gwamnati na kawo ƙarshen matsalar tsaro da ta daɗe tana hana noma, da kasuwanci, da zaman lafiya a yankin kudancin jihar. Manyan mutane, da sarakunan gargajiya, da jami’an tsaro sun halarci taron, inda suka roƙi kowa da kowa da ya tsaya kan yarjejeniyar domin amfanin kowa.
Mazauna yankin sun nuna fatan cewa wannan sabuwar yarjejeniya za ta kawo dawwamammen zaman lafiya. “Muna roƙon Allah ya tabbatar mana da wannan zaman lafiya da tsaro,” in ji wani mazaunin yankin.