A ƙalla shanu 37 ne aka ruwaito cewa ‘yan bindigar da ba a tantance su waye ba suka harbe a ƙauyen Tashek da ke ƙaramar hukumar Riyom a jihar Filato. Shugaban ƙungiyar makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN) reshen Filato, Ibrahim Babayo, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1 na rana yayin da wani makiyayi ke kiwon shanun a yankin.
Babayo ya bayyana cewa an kai wa makiyayan hari ne a yayin da suke kiwo, inda ‘yan bindigar suka ɓuya cikin dabbobin kafin su fara harbin mutane da shanu. Sai dai shugaban matasan Berom, Barista Dalyop Nwantiri, ya ce makiyayan na amfani da shanu a matsayin kariya yayin da suke kai hari ga alumnae, inda ya zargi cewa suna iya harbin kansu da dabbobinsu domin su wanke kansu daga laifin.
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Makiyayi Da Dabbobi 4 A Wani Hari A Filato
- Mijina Wayayyen Bafulatani Ne, Ba Bafulatanin Daji Ba Ne – Uwargidan Atiku
Har ila yau, wannan hari ya faru ne makonni kaɗan bayan makamancin haka da ya auku a Tanjol da Shen a ƙananan hukumomin Riyom da Jos ta Kudu. Babayo ya bayyana harin a matsayin wani yunƙuri na ɓoye wata mummunar manufa, inda ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun farmaki makiyayan da bindigogi suka kashe shanu 37 tare da raunata makiyayi ɗaya.
Bayan faruwar lamarin, Babayo ya sanar da shugaban rundunar tsaro ta musamman Operation Safe Haven da ke Riyom, inda aka fara ɗaukar matakan tsaro.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp