A ranar Juma’a da yamma, wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun tare motar haya a mararrabar Ogbabo, kan titin Itobe-Anyigba a jihar Kogi, inda suka yi awon gaba da fasinjoji 9. Direban motar da wasu fasinjoji 6 kuwa sun tsere ba tare da an sace su ba.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 4:20 na yamma a yankin ƙaramar hukumar Ofu, lokacin da ƴan bindigar suka fito daga daji suka tare titin. Sun tilasta direban motar Toyota mai ɗauke da fasinjoji tsayawa, sannan suka yi harbi cikin iska domin tsoratar da mutane. Direban motar, Sunday Okechi, ya yi dabara ya tsere tare da wasu fasinjoji 6, yayin da sauran 9 suka faɗa hannun ƴan bindigar da suka tafi da su cikin daji.
- ’Yansanda Sun Gano Gawar Ɗan Jaridar Da Aka Kashe A Jihar Kogi
- Sin Ta Yi Mu’amala Da Kasashen Dake Kan Karshen Kogin Yarlung Zangbo Dangane Da Batun Gina Tashar Samar Da Wutar Lantarki Ta Karfin Ruwa A Kogin
Nisan wurin da aka sace fasinjojin ya yi kusan mita 300 kacal daga shingen Sojoji na irin Ogbabo-Ochadamu. Jami’an tsaro sun isa wurin cikin gaggawa, inda suka tarar da motar haya mai lambar ENZ-55 XS da wata Toyota Carina ‘E’ a ajiye. An fara aikin ceto tare da haɗin gwuiwar ƴansanda, da Sojoji, da ƴan sa-kai da mafarauta domin gano masu laifin da kuma kuɓutar da waɗanda aka sace.
Kakakin rundunar ƴansanda jihar, SP Williams Ovye Aya, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa ana aiki kafaɗa da kafaɗa da sauran jami’an tsaro don ceto mutanen da aka sace tare da kama waɗanda suka aikata laifin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp