Wasu ‘yan bindiga sun sace fastoci biyu a safiyar Asabar a Jihar Adamawa. Waɗanda aka sace su ne Reverend Father Mathew David Dusami na Cocin Katolika ta Yola da Reverend Father Abraham Samman na Jihar Jalingo.
Kwamishinan Ƴansandan jihar, CP Dankombo Morris, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai yin Allah wadai da wannan aika-aika. Ya ce ‘yan bindigar sun shiga gidan ɗaya daga cikin fastocin da ke Gwaida Malam, a ƙaramar hukumar Numan, da misalin ƙarfe huɗu na asuba suka yi garkuwa da su.
- Shahararren Malamin Addinin Islama A Adamawa Sheikh Ibrahim Abubakar Daware Ya Rasu
- Na Rantse Da Allah Binani Ce Ta Lashe Zaɓen Gwamnan Adamawa A 2023 – Tsohon Kwamishinan Zaɓe
Morris ya ce an tura jami’an tsaro domin bin sawun ‘yan bindigar, tare da ƙoƙarin ceto fastocin ba tare da wata cutarwa ba. Ya kuma tabbatar da cewa ana aiki tukuru domin kama masu laifin da duk wani mai hannu a sace-sacen mutane.
Kwamishinan ya ce satar malamai abin Allah wadai ne, domin su manyan jiga-jigai ne a ƙoƙarin samar da zaman lafiya a cikin al’umma. Ya kuma buƙaci jama’a da su kwantar da hankalinsu tare da bayar da haɗin kai wajen samar da bayanai masu amfani domin ceto waɗanda aka sace da kuma kama waɗanda suka aikata laifin.