Rahotanni sun nuna cewa ana zargin sama da mutane 1,000, galibinsu mazauna ƙauyuka, na tsare a hannun ƴan bindiga a Jihar Neja, sakamakon hare-haren satar mutane da ke ci gaba da faruwa da kuma gazawar wasu iyalai wajen biyan kuɗin fansa. Wani rahoto ya ce a matsakaici, ana sace kusan mutum 20 a ƙauyukan jihar duk bayan makonni biyu, inda da dama ke ci gaba da kasancewa a hannun masu garkuwa da su.
A yankin Arewacin Neja, ƴan bindiga sun ƙara kai hare-haren satar mutane masu yawa. Rahoton ya ce ɗaya daga cikin hare-haren baya-bayan nan ya shafi kusan masu ibada 500 da aka sace daga wani masallacin Juma’a da kuma ƴan kasuwa daga kasuwar ƙauye a gundumar Dakera, dake Ƙaramar Hukumar Borgu. Haka kuma, a farkon makon nan, an sace mutane 18 a Ƙaramar Hukumar Mashegu, inda maharan suka ƙona motoci, da kasuwa da gidajen jama’a.
Sai dai Kakakin Rundunar Ƴansandan Jihar Neja, Wasiu Abiodun, ya ƙi tabbatar da adadin mutanen da ake zargin har yanzu suna tsare a hannun ƴan bindiga. Wannan ya sa ba a tabbatar da adadin sama da mutane 1,000 ɗin daga bakin rundunar ƴansanda ba.
A wani rahoto kuma, Rundunar Ƴansandan Jihar Binuwai ta ce ba ta da masaniyar wasu al’amuran satar mutane a jihar, sai dai wani sabon lamari da ya shafi limamin cocin Katolika. Kakakin rundunar, DSP Peter Orchia Aondongu, ya shaida wa jaridar Leadership Weekend cewa an sace wani limamin cocin Katolika a Ƙaramar Hukumar Ohimini, kuma jami’an tsaro sun fara ƙoƙarin ceto shi.
Rabaran. Fr. John Inalegwu Otache, na Cocin St. Margaret da ke Ajegbe-Awume, an yi garkuwa da shi ne ranar Talata, 13 ga Oktoba, 2026, a kan hanyar Otobi Amejo zuwa Ajegbe, yayin da yake dawowa daga Otukpo.
A cikin wata sanarwa, Shugaban Ofishin Gudanarwa na Diocese na Otukpo, Rabaran. Fr. Joseph Aboyi Itodo, ya ce wasu ƴan bindiga da ba a san ko su waye ba sun yi wa limamin kwanton ɓauna tare da yin awon gaba da shi. Rundunar ƴansanda ta ce jami’anta na aiki tuƙuru domin kuɓutar da shi.














