ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, October 25, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Majalisun Dokokin Jihohi Sun Fara Nazari Kan Ƙafa Ƴansanda Jiha

by Abubakar Sulaiman
1 week ago

Majalisun dokokin jihohi a faɗin Nijeriya sun fara ɗaukar matakai daban-daban kan Ƙudurin Dokar Gyaran Kundin Tsarin Mulki Karo na Shida da Majalisar Ƙasa ta aika musu, wanda ke neman halatta kafa rundunar ƴansandan jihohi (State Police). Yayin da wasu majalisun suka riga suka gudanar da karatun farko, wasu kuma na shirin fara tattaunawa da kaɗa ƙuri’a a mako mai zuwa, a daidai lokacin da ƴan tsirarun jihohi ke dakon isar ƙudurin gaban zaurensu a hukumance.

A Jihar Delta, Shugaban Majalisar Dokokin jihar kuma Shugaban Ƙungiyar Shugabannin Majalisun Dokokin Jihohin Nijeriya, Hon. Dennis Guwor, ya tabbatar da cewa majalisar za ta fara aikin duba ƙudurin dokar a ranar Talata mai zuwa, inda ya bayyana cewa ƙungiyarsu na shirin zama da Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF) domin daidaita matsayarsu kan tsarin kafin jihohi su ɗauki matsaya ta ƙarshe. Haka kuma a Jihar Kwara, jami’an majalisar sun tabbatar da cewa ƙudurin na samun cikakkiyar kulawa, kuma ana sa ran za a gabatar da shi a zauren majalisar domin tattaunawa da yiwuwar zartar da shi da zarar sun dawo zama a ranar Talata.

A shiyyar Arewa ta Tsakiya, Majalisun Dokokin Jihohin Neja da Benue sun samu nasarar gudanar da karatun farko (first reading) na ƙudurin a zauren majalisunsu biyo bayan dawowa daga hutu, yayin da a Jihar Filato, Shugaban Majalisa Rt. Hon. Naanlong Daniel ya bayar da umarnin hanzarta duba ƙudurin bayan Gwamna Caleb Mutfwang ya miƙa shi. Daniel ya jaddada cewa kafa ƴansandan jihohi zai taimaka matuƙa wajen magance rikice-rikicen tsaro da hare-haren da ke addabar al’ummomin Mangu, da Bokkos, da Barkin Ladi.

ADVERTISEMENT

Dangane da yankunan Kudu maso Yamma da Kudu maso Gabas kuwa, Majalisar Dokokin Jihar Ondo ta miƙa ƙudurin ga Kwamitin Daukacin Majalisa (Committee of the Whole) domin bai wa dukkan ƴan majalisa damar tofa albarkacin bakinsu a maimakon barin sa ga kwamiti na musamman. A Jihar Imo kuma, majalisar ƙarƙashin jagorancin Hon. Chike Olemgbe ta karɓi ƙudurin inda ta tura shi ga kwamitocin shari’a da yaɗa labarai domin nazari sosai kafin a kaɗa ƙuri’ar amincewa.

Sai dai kuma, a jihohi irin su Akwa Ibom da Enugu, jami’an majalisa sun bayyana cewa har yanzu ƙudurin bai isa gaban zauren majalisun ba domin fara tattaunawa a kansa. Wannan shiri na sauya fasalin tsarin tsaro a ƙarƙashin sashi na 9 na Kundin Tsarin Mulkin 1999 na buƙatar samun amincewar aƙalla kashi biyu cikin uku na majalisun dokokin jihohi 36 na ƙasar kafin ya zama doka, matakin da ake sa ran zai kawo gagarumin sauyi ga harkokin tsaron cikin gida a Nijeriya.

LABARAI MASU NASABA

Wa’adin INEC Ya Ƙare: Ina Makomar Takarar Aminu Gwarzo A Kano Da Pantami A Gombe?

Sojoji Sun Kuɓutar Da Mutane Uku Da Aka Sace A Kebbi

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Mafarauta Sun Kashe Ƴan Bindiga 14, Sun Kuɓutar Da Mutane 3 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Katsina
  • Abubakar Sulaiman
    Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 10 A Taraba, Sun Kwashi Kayan Abinci
  • Abubakar Sulaiman
    Gwamnatin Kaduna Ta Musanta Zargin Kashe Tiriliyan 2.3 Kan Gangamin APC
  • Abubakar Sulaiman
    Taron Kaduna Ya Tabbatar Da Goyon Bayan Arewa Maso Yamma Ga Tinubu — Musa Iliyasu

MASU ALAKA

Wa’adin INEC Ya Ƙare: Ina Makomar Takarar Aminu Gwarzo A Kano Da Pantami A Gombe?
Siyasa

Wa’adin INEC Ya Ƙare: Ina Makomar Takarar Aminu Gwarzo A Kano Da Pantami A Gombe?

October 25, 2026
Sojoji Sun Kuɓutar Da Mutane Uku Da Aka Sace A Kebbi
Tsaro

Sojoji Sun Kuɓutar Da Mutane Uku Da Aka Sace A Kebbi

October 25, 2026
Ana Buƙatar Ɗaukar Matakai Masu Tsauri Domin Ci Gaban Nijeriya – Wike
Labarai

Ana Buƙatar Ɗaukar Matakai Masu Tsauri Domin Ci Gaban Nijeriya – Wike

October 25, 2026
Next Post
Sojoji Sun Kashe Ƴan Ta’adda 11, Sun Cafke 22 Tare Da Ceto Mutane 25

Rundunar Sojin Nijeriya Ta Tura Dakarunta Yaƙi Da ‘Yan Bindiga A Yankin Olle-Bunu Na Jihar Kogi

Sojoji Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 15 Ta Harin Sama A Borno

October 25, 2026
2027: Hana Tinubu Wa’adi Na Biyu Na Iya Jefa Nijeriya Cikin Rikicin Siyasa — Pakistan

Tinubu Ya Cancanci A Sake Zaɓensa A 2027 — Pakistan

October 25, 2026
Amnesty Ta Yi Allah Wadai Da Harin Jihar Taraba Da Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 40

Amnesty Ta Yi Allah Wadai Da Harin Jihar Taraba Da Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 40

October 25, 2026
Kwamitin Zartarwa Na ADC Na Ƙasa Ya Yi Watsi Da Bangaran David Mark Da Bala Gombe, Ya Naɗa Shugabancin Riƙo

ADC Ta Yi Wa APC Ba’a Kan Zargin Hayar Taron Jama’a Da Rashin Cika Kujeru A Taron Kaduna

October 25, 2026
An Yi Wa Tinubu Ihun “Ba Ma Yi” A Taron Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen APC A Kaduna

An Yi Wa Tinubu Ihun “Ba Ma Yi” A Taron Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen APC A Kaduna

October 24, 2026
Sin Ta Lashe Lambobin Yabo Mafiya Yawa A Gasar Asiya Ta 2026 Ajin Masu Bukatar Musamman

Sin Ta Lashe Lambobin Yabo Mafiya Yawa A Gasar Asiya Ta 2026 Ajin Masu Bukatar Musamman

October 24, 2026
EUROMATCH NPFL: Katsina United Ta Raba Maki Da Plateau United

EUROMATCH NPFL: Katsina United Ta Raba Maki Da Plateau United

October 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.